Na daina zuwa makarantar Islamiyya ne saboda bulalar Malam – Obasanjo

Na daina zuwa makarantar Islamiyya ne saboda bulalar Malam – Obasanjo

Tsohon shugaban kasa Olusegun Obasanjo ya bayyana ‘bulalan Malam’ a matsayin babban kalubalen daya fuskanta wajen neman ilimin addinin Musulunci a yayin da yake zuwa makarantar Islamiyya.

Jaridar Sahara Reporters ta ruwaito Obasanjo ya bayyana haka ne yayin wani taron kulla kyakkyawar dangantaka tsakanin Musulmai da Kirista da aka shirya a garin Abekouta na jahar Ogun, inda yace yana zuwa Islamiyya kullum a lokacin da yake yaro, amma yawan bulala yasa ya tsere.

KU KARANTA: Gwamnatin Ganduje ta garkame wani babban banki saboda bashin N423m

A jawabinsa, Obasanjo ya yi kira ga yan Najeriya dasu zauna lafiya da junansa, tare da hada kai domin cigaban kasa, ya kara da cewa da Najeriya ta wuce haka idan da a ce Musulmai da Kiristoci sun zauna lafiya da junansu.

“Idan da a ce zamu zauna lafiya da makwabtanmu, a matakin unguwanni, jaha, kasa, nahiya da kuma duniyar gaba daya da mun samar da kyakkyawar duniya abar sha’awa. Bari ku ji, ina zuwa Islamiyya a kauyenmu domin a kauyenmu an hada Coci da Masallaci a wuri daya ne.

“Da nake yaro a kauyenmu babu wani bambanci, don haka sai na fara zuwa makarantar Islamiyyah, amma babban abin da ya koreni daga sallame ni daga Islamiyyah shi ne bulalan Malam, amma abin da na koya a kauye yayin da nake girma shi nake dabbakawa a rayuwana har yanzu.” Inji shi.

Idan za’a tuna a makon da ta gabata ne tsohon shugaban kasa Obasanjo ya kai ziyara ga gwamnan jahar Kaduna, Malam Nasir Ahmad El-Rufai inda ya bayyana gwamnan a matsayin hazikin mutum wanda zai iya duk aikin da aka bashi.

Sai dai jama’a da dama sun fassara ziyarar da tsohon shugaban ya kai ma gwamnan, musamman duba da rashin jituwa dake tsakaninsa da gwamnan a shekarun baya, don haka suke ganin yana da wata manufa ko bukata da yake nema a wajen gwamnan.

Ku biyo mu a https://facebook.com/legitnghausa

ko a http://twitter.com/legitnghausa

KU LATSA: Hanyar sauko da sabuwar manhajar jaridar Legit.com Hausa cikin sauki

Ga masu shawara ko korafi, a same mu a labaranhausa@corp.legit.com

Sanarwa na musamman: Shafin NAIJ Hausa ya koma Legit Hausa

Source: Legit

Online view pixel