Zamfara: Dan takarar gwamna a jam'iyyar PDP ya koma APC

Zamfara: Dan takarar gwamna a jam'iyyar PDP ya koma APC

Shugaban jam'iyyar APC na yankin Zamfara ya tabbatar da cewa sun samu sabon mamba a jam'iyyar. Sani Gwamna ya bayyana cewa sun samu dan jam'iyyar PDP wanda ya yi takarar neman tikitin fitowa zaben gwamnan jihar a jam'iyyar.

Sani Gwamna ya bayyana yadda Shehu Bakauye ya sauya sheka zuwa jam'iyyar APC, bayan taron da jiga-jigan jam'iyyar suka yi a jihar, kamar yadda Kamfanin Dillancin Labarai ya ruwaito.

Bakauye ya fito neman kujerar gwamnan jihar karkashin inuwar jam'iyyar PDP amma Gwamna Bello Matawalle ya maka shi da kasa a yayin zaben fidda gwani.

"A yau ne Shehu Bakauye da wasu magoya bayansa suka hadu. Sun amince shawo kan banbance-banbancen da ke tsakaninsu tare da alkawarin aiki tare a siyasance", ya ce.

DUBA WANNAN: Abun da yasa muke yi wa jama'a rijista - Gwamnatin jihar Kaduna

Shugaban jam'iyyar APC din na jihar Zamfara, Lawal Liman, ya kwatanta wannan sauya shekar da cigaba abun maraba.

Ya ce, jam'iyyar tuni ta fada neman tattaunawa da fusatattun 'yan jam'iyyar don samun sasanci a kan abinda ya afkawa jam'iyyar a jihar.

Ya kara da rokon mambobin jam'iyyar a jihar da su kwantar da hankalinsu, tare da cigaba da zama tsintsiya madauri daya. Ya bukacesu da su kasance masu bin doka sau da kafa.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit.ng

Online view pixel