Yadda mijin mahaifiyata ya nemi lalata dani lokacin da nake dauke da ciki - Jaruma

Yadda mijin mahaifiyata ya nemi lalata dani lokacin da nake dauke da ciki - Jaruma

- A ranar Laraba ne wata ma’aikaciyar gidan Talabijin ta yi murnar zagayowar ranar rabuwarta da mijinta

- Tsohon mijin ya je tare da mayar mata da martanin yadda ta aureshi don kudi kuma ya kamata da bature

- Tuni ta karyata hakan tare da fallasa dalilin rabuwarsu na cewa, mahaifinshi ne ke nemanta da lalata

A ranar Laraba 18 ga watan Disamba ne wata ma’aikaciyar gidan talabijin mai suna Juliet Mgborukwe ta yi bikin murnar rabuwa da mijinta mai suna Chima Ojukwu.

Ganin wannan bikin murnar ne yasa tsohon mijin nata din ya wallafa rubutun mayar da martani. Ya bayyana cewa ta aureshi ne saboda kudinshi wanda kuma bata samu ba. Ya bayyana yadda ya kama ta da wani bature suna lalata.

Bayan wannan fallasar ne kuwa shafin SDK ya tuntubeta don jin ta bakin ta. A nan ne kuwa ta bude sirrin abinda ya raba su.

Kamar yadda ta ce, “Ikirarin da yayi na cewa ya kama ni da wani bature duk karya ne. A takaice ma dariya nayi. A lokacin da nake da ciki, iyayenshi na zama tare da mu saboda tsananin talaucinsu. Ba zasu iya kama gida su kadai ba.

KU KARANTA: Kaddara ce idan ka tashi ka tsinci kanka a matsayin dan Najeriya - Sarkin Musulmi

“Mahaifinshi ya dinga nema na amma naki amincewa dashi. Fadanmu ya fara ne lokacin da na sanar dashi cewa mahaifinshi na nemana duk da ina da ciki. Don a duk lokacin da ya fita aiki, sai ya dinga neman shawo kaina don in amince dashi.

“Na yi kuskuren fadawa hannun mai dukan mata. Ya dake ni amma bai isa ya hana ni cikar burikana ba. Bai isa ya kashe karfin zuciyar da nake da shi ba. Ba zan yi shiru yana shirya karairayi a kaina.”

A tambayar Juliet da aka yi sahihancin zancenshi da ya ce saboda kudinshi ta aure shi, ta ce “Kada ku damu da surkullenshi. Shekarunshi 20 a Amuka amma bai iya siyen ko gidan kanshi ba har sai da naje kasar. A halin yanzu ya siyar da gidan kuma kotu ta sa shi ya dinga biyana don gidan nawa ne.”

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel