Kaddara ce idan ka tashi ka tsinci kanka a matsayin dan Najeriya - Sarkin Musulmi

Kaddara ce idan ka tashi ka tsinci kanka a matsayin dan Najeriya - Sarkin Musulmi

- Sarkin musulmai kuma shugaban majalisar koli ta addinin musulunci, ya bayyana bukatar sauya alkiblar kasar nan

- Sarkin musulmin ya bayyana damuwarshi ta yadda ‘yan kasa daya basu kallon juna a matsayin ‘yan uwa

- Ya bayyana yadda ya guji saka kanshi ko bakinshi a lamurran zabe, saboda shi shugaban addini ne

Sarkin musulmai kuma shugaban majalisar koli ta al’amuran addinin musulunci, Sa’ad Abubakar ya bayyana cewa alkiblar da kasar nan ke fuskanta na da matukar hatsari. Ya bayyana cewa, talaka na da hujjar fusata tun daga yadda aka yi zaben wannan shekarar.

Sarkin musulmin ya bayyana tsananin damuwarshi yayin taron kungiyar kula da da’awah ta Najeriya da aka yi a fadarshi ta shekarar 2019. Ya bayyana cewa, abun haushi ne ta yadda muna ‘yan kasa daya amma bamu kallon juna a matsayin ‘yan uwa. Ya kara da koka wa kan yadda aka mayar da majami’u da masallatai wajen siyasa ba wajen bauta ba.

“Yan uwan juna a halin yanzu sai ka tsincesu suna gaba. Abokai sun rabu saboda matsalolin da suka fuskanta na banbancin ra’ayi kafin zabe. Makwabta sun tsani juna saboda ba jam’iyyarsu ba daya ba,” yace.

Sarkin musulmin ya bayyana yadda zaben 2019 ya cika da banbance-banbancen addini daga shuwagabannin addinai. Ya yi kira garesu da su kasance marasa goyon bayan kowa.

KU KARANTA: Sai hakuri abin a jinina ne, bazan iya dainawa ba - In ji matar da aka kama ta kwanta da maza 100

Shugaban addinin ya bayyana cewa, duk da zaben ya kasance ne tsakanin ‘yan takara biyu kuma dukkansu musulmai ne, wasu daga cikin shuwagabannin addinan sun mayar da wajen bauta dakunan taron siyasa.

Ya jaddada cewa: “A matsayinmu na shuwagabannin addinai, ya kamata mu yi taka tsan-tsan a kan abinda muke sanar da mabiyanmu saboda wasu daga cikinsu basu da ilimi. Abinda muka sanar dasu shine abinda suke bi. Na kasance mai kallon yadda ake gudanar da zabuka tuntuni. Amma ban taba fitowa na sanar da cewa ga dan takarata ba.”

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit.ng

Online view pixel