Akwai yiwuwar Boko Haram ta yi amfani da makamai masu guba a nan gaba - FG

Akwai yiwuwar Boko Haram ta yi amfani da makamai masu guba a nan gaba - FG

- Gwamnatin Najeriya ta ce akwai alamu da ke nuna cewa yan ta’addan Boko Haram na iya kai hari da makamai masu guba

- Hakan na kunshe ne a cikin takada mai shafi 60 mai taken “National Security Strategy” wato “Dabaran tsaron kasa”, wanda ofishin mai ba kasa shawara a harkar tsaro ta saki

- A kokarinta na magance hakan, gwamnatin tarayya ta mayar a hankali sosai a hadin gwiwa tsakanin hukumomin tsaro domin dakile kokarin yan ta’addan

Gwamnatin tarayya ta ce akwai alamu da ke nuna cewa yan ta’addan Boko Haram na iya kai hari da makamai masu guba wadanda ake kira da chemical, biological, radiological, nuclear and explosive (CBRNE) a nan gaba.

A cewar jaridar Punch, hakan na kunshe ne a cikin takada mai shafi 60 mai taken “National Security Strategy” wato “Dabaran tsaron kasa”, wanda ofishin mai ba kasa shawara a harkar tsaro ta saki a baya.

Takardar, wanda Shugaban kasa Muhammadu Buhari ya rubuta farkonsa, ya mayar a hankali kan bukatar karin harin kai a tsakanin hukumomin tsaro domin magance matsalolin tsaro a kasar.

An tattaro cewa kungiyar yan ta’addan ISIS, wacce ke da hadin gwiwa a Boko Haram, na neman hanyar mallakar makaman CBRNE.

An kawo cewa idan har ISIS ta mallaki makaman, Boko Haram ba za ta daina kwasarsu ba a hare-harenta.

KU KARANTA KUMA: Wasu Kiristocin Arewa sun roki Shugaba Buhari ya kubuto da Leah Sharibu

A wani kokari na magance hakan, dabarar Najeriya ta mayar a hankali sosai a hadin gwiwa tsakanin hukumomin tsaro domin dakile kokarin yan ta’addan.

A cewar takardar, kasar za ta karfafa tsarin kudin kasar sannan ta hada kai da tsarin kasa da kasa wajen bibiyar masu daukar nauyin yan ta’adda.

A wani labari na daban, Legit.ng ta rahoto cewa Fadar gwamnatin Najeriya ta bayyana cewa wasu manyan mutane a Najeriya na yaki da shugaban kasa Muhammadu Buhari ne ba don komai ba sai don kawai ya hanasu lasisin mallakar rijiyoyin mai.

Mai magana da yawun shugaban kasa, Garba Shehu ne ya bayyana haka yayin da yake ganawa da manema labaru a Villa, inda yace suna sane da takun da manya a Najeriya suke yi, kuma walki suke daidai da kugun kowa.

Idan ku na da wata shawara ko bukatar bamu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewa tare da mu.

Asali: Legit.ng

Online view pixel