Dattawan arewa: An fara sulhu tsakanin Ganduje da Sanusi

Dattawan arewa: An fara sulhu tsakanin Ganduje da Sanusi

Zauren dattawan Arewa wacce aka fi sani da Northern Elders Forum (NEF), ta fara wani taro domin sasanci a tsakanin Gwamna Abdullahi Umar Ganduje da kuma fadar Sarkin Kano Muhammadu Sanusi II.

Dattawan sun yi yunkurin sulhu tsakanin Gwamnan da Sarkin ne bayan da Sarkin ya amince da nadin da gwamnan Kano yayi masa, na shugaban majalisar sarakunan jihar.

Sanusi ya amince da nadin ne bayan da aka aike masa da wasikar neman ko dai ya amince ko kuma akasin hakan, biyo bayan shirun da ya yi tun farko.

Dr. Hakeem Baba Ahmed na kungiyar NEF ya shaida wa BBC cewa, kasancewarsu dattawa, ba dai-dai bane suna ganin wannan lamarin na faruwa, kuma su ja bakinsu su yi shiru.

DUBA WANNAN: Zargin maita: Mahaifi ya bankawa 'ya'yansa biyu wuta

"Mun tara dattijan Arewa daga ko ina domin samun kawo karshen hayaniyar da muka ji ana yi," Hakeem ya ce.

Ya ci gaba da cewa: "Ba tun yau muke maganar ba, ji ne kawai ba a yi. Sai da muka tabbatar mun samu izinin duk wadanda abin ya shafa sannan muka zo.

"Abinda kafafen yada labarai suke sanarwa ba shine yake faruwa ba, don ba haka muka tarar ba. Da muka samu sauraron kaman gwamnati da masarauta sai muka fahimci cewa ba wani abu bane da za a samu matsala a kai ba.

"Ba ma fatan abin da zai taba Kano domin kuwa muna da matsaloli masu tarin yawa a Arewa. Wannan lamarin kuwa zai iya kara wa matsalolin yawa.

"Muna godiya ga Allah don ba a boye mana komai ba. Komai da muka ji ya yi mana amfani kuma muna so duk abinda za a yi ya kasance bisa ga al'adunmu na Arewa."

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit

Online view pixel