Gwamnonin arewa uku da suka kara aure bayan sunci zaben 2019

Gwamnonin arewa uku da suka kara aure bayan sunci zaben 2019

A kalla gwamnoni uku ne a arewa suka kara aure bayan nasarar da suka samu a zabukan 2019 da aka yi. Wadannan gwamnonin sun kara aure ne kamar yadda addinin Islama ya tanadar. Biyu daga cikinsu gwamnonin APC ne inda guda daya kacal ne na PDP.

Su waye gwamnonin nan?

1. Abdullahi Sule

Zababben gwamnan jihar Nasarawa ne. Injiniya Abdu Sule ya auri sabuwar amaryarsa ne jim kadan bayan nasarar lashe zaben kujerar gwamnan jihar Nasarawa da yayi. Ya auri Hajiya Farida Salisu Ali daga jihar Katsina.

Anyi auren ne a watan Afirilu a wata ranar Juma'a. Mai magana da yawun gwamnan ne ya sanar da hakan. Amma kuma, matar gwamna ta farko, Silifat Sule ce ke rike da ofishin uwargidan gwamnan tun daga watan Mayu.

Gwamnonin arewa uku da suka kara aure bayan sunci zaben 2019

Gwamnan jihar Nasarawa
Source: UGC

2. Bala Mohammed

Sanata Bala Mohammed mai shekaru 61 ya kara sabuwar amarya ne mai suna Natasha Mariana, 'yar asalin kasar Lebanoon amma a Najeriya ta girma. An yi auren ne a sirrance a Ikoyi, jihar Legas a ranar Juma'a 16 ga watan Yuli, 2019.

Anyi auren ne bayan watanni biyu da gwamnan ya hau mulkin jihar Bauchi. Bala na tare da matarsa mai suna Aishatu Mohammed wacce Allah ya albarkacesu da 'ya'ya 16.

Gwamnonin arewa uku da suka kara aure bayan sunci zaben 2019

Gwamna Bala Mohammed da amaryarsa
Source: UGC

DUBA WANNAN: Soyayya: Ahmed Indimi da Zahra Buhari sun yi murnar cikar shekara uku da aure (Hotuna)

3. Mai Mala Buni

Sa'o'i kadan bayan da ya karba rantsuwa a matsayin gwamnan jihar Yobe, Mai Mala Buni ya auri 'yar gwamnan da ya gada, Adama Ibrahim Gaidam. A halin yanzu Adama na karatu ne kasar Saudi Arabia.

Anyi auren gwamnan da Adama ne a gidan tsohon gwamnan kuma mahaifinta dake Sabon Fegi a Damaturu. Kamar yadda labarai suka nuna, tuntuni suna soyayya amma an boye ne saboda wasu dalilai.

Gwamnonin arewa uku da suka kara aure bayan sunci zaben 2019

Mai Mala Buni - Gwamnan jihar Yobe
Source: Twitter

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit

Online view pixel