Soyayya: Ahmed Indimi da Zahra Buhari sun yi murnar cikar shekara uku da aure (Hotuna)

Soyayya: Ahmed Indimi da Zahra Buhari sun yi murnar cikar shekara uku da aure (Hotuna)

A halin yanzu shekaru uku kenan da auren 'yar shugaban kasa Muhammadu Buhari, Zahra da Ahmed Indimi. Masoyan junan sun yi murnar zagayowar wannan ranar, da kalaman soyayya ga juna. Sun garzaya shafinsu na Instagram a ranar Litinin don murnar. A nan kuma suka bayyana hotuna da kalaman soyayya.

Soyayya: Ahmed Indimi da Zahra Buhari sun yi murnar cikar shekara uku da aure (Hotuna)
Zahra Indimi
Asali: Twitter

Ahmed ya rubuta: "Gareki matata. Nagode da lokaci mai matukar tarihi da muka yi rayuwa a tare. Kin bani sabon dalili na rayuwa: Abar kaunata, ina ma kyakyawar matata murnar zagayowar ranar aurenmu."

DUBA WANNAN: Kasafin kudi: Buhari ya kafa sabon tarihi - Gwamnonin APC

A bangaren Zahra kuwa, ta wallafa kalaman nata kamar haka: "A yau shekaru uku kenan masu matukar amfani da muka yi tare. Ubangiji ya albarkaci zuciyarka masoyina. Ka zama babbar kyauta gareni daga Allah. Ina mika godiyata ga Ubangiji a kan wannan rahamar da yayi min,

Soyayya: Ahmed Indimi da Zahra Buhari sun yi murnar cikar shekara uku da aure (Hotuna)
Zahra Indimi
Asali: Instagram

"Ina matukar godiya ga Ubangiji da Allah ya hada zukatanmu. Ina godiya ga Ubangiji da ya bani hakuri har muka kai inda muke a yanzu. Barka da shekarun da suka gabata."

Muna musu fatan shekaru masu albarka cike da so da kaunar juna.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Authors:
Mudathir Ishaq avatar

Mudathir Ishaq Mudathir Ishaq is the head of the Hausa desk at Legit.ng. He studied Industrial Chemistry as first degree at the University of Abuja, Journalism (CSR Specialization) with the Michigan State University and runs MSc Industrial Chemistry from the Nasarawa State University, Keffi. With more than a decade experience in news reporting and content editing, he has interviewed influential personalities. He can be reached on: mudathir.ishaq@corp.legit.ng