Abin kunya: Magidanci ya dirka ma diyarsa cikin shege, ya zubar da abin sa
Wani magaidanci mai matsakaicin shekaru kuma mamuguncin uba ya dirka ma diyarsa yar shekara 16 cikin shege a jahar Ogun, sa’annan daga bisani ya nemi taimakon wani mai maganin gargajiya wajen zubar da cikin.
Jaridar Daily Trust ta ruwaito sunan wannan mugun mutumi Taofeek Oyeyemi kamar yadda mai magana da yawun rundunar Yansandan jahar Ogun, DSP Abindola Oyeyemi ta bayyana, inda tace sun samu nasarar kama shi ne bayan mahaifiyar yarinyar ta kai kara zuwa caji ofis dake Ewekoro.
KU KARANTA: Kaico! Kasa ta danne kananan yara 3 da ransu a garin Kaduna, sun sheka barzahu
Mahaifiyar yarinyar ta bayyana ma Yansandan cewa diyarta da take zama da tsohon mijinta ta tabbatar mata da cewa mahaifinta ya dirka mata cikin shege, sa’annan kuma har ya dauketa ya kai ta zuwa wurin wani mai maganin gargajiya domin a zubar da cikin.
Sai dai kash! Tun bayan da aka zubar da wannan ciki, yarinyar ba ta daina zubar da jini ba, kamar yadda mahaifiyar ta fallasa mahaifin yarinyar a wajen jami’an ofishin rundunar Yansanda dake Ewekoro.
“Samun wannan rahoto yasa DPO na Yansandan yankin, SP Rotimi Jeje ya umarci jami’ansa su kamo masa wanda ake tuhuma, haka kuma aka yi, cikin sauki suka kamo shi tare da taso keyarsa.
“A nan mahaifin yarinyar wanda ya bayyana cewa yana da yara 17 daga aure da dama da ya yi, ya tabbatar ma Yansanda cewa tabbas yana kwanciya da diyarsa, kuma shi ya dirka mata ciki, amma ya zubar da cikin don kada asirinsa ya tonu.” Inji kaakakin Yansandan.
Binciken Yansanda ya gano yarinyar tana zama tare da mahaifyarta ne tun bayan rabuwar aurensu da mahaifinta, amma kimanin watanni 6 da suka gabata ya kwace yarinyar ya mayar da ita gidansa, har sai wannan rana da mahaifiyar ta ziyarci diyar, a lokacin ta gano halin da yarinyar take ciki.
Daga karshe kwamishinan Yansandan jahar, CP Kenneth Ebrimson ya bada umarnin a mika shi zuwa sashin binciken laifukan da suka shafi cin zarafin yara da domin gudanar da cikakken bincike tare da gurfanar da shi gaban kotu.
Ku biyo mu a https://facebook.com/legitnghausa
ko a http://twitter.com/legitnghausa
KU LATSA: Hanyar sauko da sabuwar manhajar jaridar Legit.com Hausa cikin sauki
Ga masu shawara ko korafi, a same mu a labaranhausa@corp.legit.com
Sanarwa na musamman: Shafin NAIJ Hausa ya koma Legit Hausa
Asali: Legit.ng