Kusma Vati: Tsohuwar da ta shafe sama da shekaru 60 tana cin kasa da duwatsu ba tare da sun yi mata illa ba

Kusma Vati: Tsohuwar da ta shafe sama da shekaru 60 tana cin kasa da duwatsu ba tare da sun yi mata illa ba

- Kusma Vati tsohuwa ce mai shekaru 80 a duniya wacce take rayuwa a kasar Indiya

- Vati ta dau shekaru 65 na rayuwarta tana cin kasa da yashi, don kuwa ta ce shi ke bata karfi

- Ta bayyana cewa, bai taba mata illa ba don ta dade rabonta da rashin lafiya. Yana ba hakorinta karfi sosai

Idan da mai karatu zai tambaya kakaninshi sirrin doguwar rayuwa, akwai tabbacin ba zasu kira kasa da yashi ba a cikin jerin.

Amma kuma, Kusma Vati daga Varanasi mai shekaru 80 a kasar Indiya, ta tabbatar da cewa cin kasa da yashi da takeyi ne yasa ta tsawon rayuwa.

Kamar yadda ta bayyana, tana da shekaru 15 kacal a duniya lokacin da ta fara cin kasa sakamakon ciwon cikin da ya dameta. Daga nan ne kuwa bata waiwaya ba, ta cigaba da cin kasa da yashi a matsayin abincinta.

Kusma Vati: Tsohuwar da ta shafe sama da shekaru 60 tana cin kasa da duwatsu ba tare da sun yi mata illa ba
Kusma Vati: Tsohuwar da ta shafe sama da shekaru 60 tana cin kasa da duwatsu ba tare da sun yi mata illa ba
Asali: Facebook

Mutane da yawa, har da jikokinta sun damu da illar da wannan abinci nata zai iya yi ga lafiyarta. Amma ta yadda cewa, tauna kasa da yashin na kara wa hakoranta karfi. Ta bayyana cewa, zata iya cizon dutse mafi karfi.

"Na kasance mai cin kasa da yashi kusan shekaru 63 da suka gabata. A halin yanzu inason abinda nake yi kuma bana tunanin yana da illa.

"Ban taba samun wata matsala a cikina ba ko baki ko kuma hakorana ba. Sai ma kara musu karfi da hakan ya yi. Zan iya cizon dutse mai matukar karfi."

Kusma Vati: Tsohuwar da ta shafe sama da shekaru 60 tana cin kasa da duwatsu ba tare da sun yi mata illa ba
Kusma Vati: Tsohuwar da ta shafe sama da shekaru 60 tana cin kasa da duwatsu ba tare da sun yi mata illa ba
Asali: Facebook

KU KARANTA: Yanzu-yanzu: Majalisar kasar Amurka ta tsige shugaba Donald Trump

Jikokinta sun so hanata amma sai ta ce sinadaran da ke ciki ne ke kara mata lafiya.

Ta ce: "Jikokina sun so inje a duba min lafiyata amma ni ban ga bukatar hakan ba. Ina da lafiya kuma garau nake. Ina matukar godiya ga kasa, wacce itace sirrin lafiyata."

"Na dade banyi ciwo ba gaskiya. Inajin lafiya sosai a jikina. Sinadaren dake cikin kasar ne ke bani karfin aiki a gonata."

Kusma Vati: Tsohuwar da ta shafe sama da shekaru 60 tana cin kasa da duwatsu ba tare da sun yi mata illa ba
Kusma Vati: Tsohuwar da ta shafe sama da shekaru 60 tana cin kasa da duwatsu ba tare da sun yi mata illa ba
Asali: Facebook

Vati tana fara tara kasar da yashin a tukunyar kasa sannan ta barsu su bushe kafin ta fara ci.

Vati ta saba da cin kasar da yashin don kuwa ta kan dauka lokaci tana neman irin kasar da take ci.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel