Hotunan wasu mawaka da hadimin gwamnan Kebbi ya sa aka lakada musu dan banzan duka
Wasu mawaka su 8 sun shiga tasku yayin da wani hadimin gwamnan jahar Kebbi yasa aka lakada musu dan banzan duka a gabansa tare da barazanar kashe guda daga cikinsu saboda sun yi wata waka dake shagube ga Gwamna Abubakar Bagudu.
Jaridar Sahara Reporters ta ruwaito hadimin mai suna Faruku Musa Yaro Enabo ne yasa aka kamo mawakan inda aka gazaya dasu zuwa gidansa, sa’annan yasa katti suka dinga jibgarsu a cikin gidan nasa.
KU KARANTA: Har yanzu da sauran aiki kan batun kawar da talauci a Najeriya – Osinbajo
Mawakan sun hada da; Kabiru Azila (KB Show), Ayuba Ibrahim, Musa Alle, Bello Ajannare, Shamsu Attahitu Otono da wasu guda uku da ba’a bayyana sunayensu ba, wanda hadimin gwamnan ke tuhumarsu da rera wata wakar sukar gwamnatin Bagudu.
Da yake bayyana yadda lamarin ya auku, Arzila yace su hudu aka fara kamawa a Hotel din Abacha da misalin karfe 3:30 na daren Litinin. “Wasu mutane 10 ne suka kamamu suka kaimu gidan Faruku Musa, da gaske mun yi wakar suka ga gwamnatin jahar Kebbi, amma a matsayinmu na yan jahar Kebbi hakkinmu ne mu soki mulkin kama karya da ake mana a jahar.
“Ba zamu yi shiru ba yayin da Gwamna Bagudu ke cigaba da lalata mana jaha da rashin iya mulki, sai dai bamu taba tunanin zasu kai ga cin zarafinmu ba. A gidan Faruku ne yasa wasu kattai suka dinga jibgarmu wai har sai mun fada masa wa ya bamu umarnin yin wakar.
“Har sai daya dauko bindigar AK 47 ya yi barazanar kashe Bello Aljannare, daga nan ya gargademu kada mu sake rera wata waka ta zagin gwamnan Kebbi ko wani jami’in gwamnatin jahar, sa’annan ya sakemu.” Inji shi.
Babban daraktan wata kungiya mai zaman kanta, Kebbi Concern Citizens, Ibrahim Muhammad ya tabbatar da aukuwar lamarin bayan ya ziyarci mawakan a asibiti, sai dai Faruku Yaro yaki yin magana da majiyarmu a lokacin da ta tuntubeshi game da lamarin.
Ku biyo mu a https://facebook.com/legitnghausa
ko a http://twitter.com/legitnghausa
KU LATSA: Hanyar sauko da sabuwar manhajar jaridar Legit.com Hausa cikin sauki
Ga masu shawara ko korafi, a same mu a labaranhausa@corp.legit.com
Sanarwa na musamman: Shafin NAIJ Hausa ya koma Legit Hausa
Asali: Legit.ng