Kyakkyawar budurwar da take biya kanta kudin makaranta ta hanyar yin aikin gini ta kammala karatun ta na jami'a

Kyakkyawar budurwar da take biya kanta kudin makaranta ta hanyar yin aikin gini ta kammala karatun ta na jami'a

- Nfai Eunice Tayemiyar kyakkyawar matashiyar budurwa ce wacce ta kammala digirinta na biyu

- Tayemiyar ta kammala digirinta na biyu ne daga jami’ar kimiyya da fasaha ta Kwame Nkrumah

- Daga yankin Arewacin kasar Ghana, ta bayyana yadda ta dinga fafutuka don kokarin kammala karatun

Idan aka haifeka a yankin karkara na arewacin kasar Ghana, dole ne ki iya girki kuma makomarki na madafi ne.

Wannan ne labarin wata matashiyar budurwar da ta kammala digirinta na biyu a kasar Ghana. Amma ita ba hakan bane ya faru da ita.

Nfaia Eunice Tayemiyar ta shiga cikin jerin labaran karfafa guiwa da jaridar Legit.ng ta ruwaito a 2019.

Duk da cewa an haifeta a yankin da ake hana karatu kuma karkara a kasar Ghana, Nfai Eunice Tayemiyar, ta kalubalanci yanayin yankinta kuma ta shawo kan rashin kudin da ka iya kawo kalubale ga karatunta.

Wahalar daukar nauyin kanta da ta karatunta ya rataya ne a kanta tun tana da shekaru 12 bayan da kakarta ta kwanta dama. Mahaifinta ya yi nisa da ita tun bayan da ya auri sabuwar amaryarshi.

KU KARANTA: Ran matar aure ya baci ta bada lambar wayarta ga duk mai son lalata da ita, bayan ta kama mijinta yana iskanci da wata

Ta fara ne da daukar kankare tare da sauran kananan aiyuka, ta hakan ne take samun yadda zata biya wa kanta kudin makaranta. A matsayinta na mai kananan shekaru, ta yi wa kanta rijistar jarabawar BECE bayan da mahaifinta ya sanar da ita ba zai iya biya mata ba.

A matsayinta na mai digiri har biyu, ta rubuta: “A matsayin wacce aka haifa a karkara a kasar Ghana. An haifeni a gidan da ke da talauci, mahaifiyata ta rasu kuma kakata da ke rainona ta rasu lokacin da nake da shekaru 12 a duniya. Mahaifina ya tare da sabuwar amaryarshi kuma bai damu da karatuna ba. Da kaina na dau nauyin kaina don har daukar kankare nakeyi. A haka na kai inda nake kuma ina tunkaho da hakan.”

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit

Online view pixel