Tirkashi: Ango ya nemi a raba aurenshi da matarsa, bayan tana tsula masa fitsarin kwance a gado kullum

Tirkashi: Ango ya nemi a raba aurenshi da matarsa, bayan tana tsula masa fitsarin kwance a gado kullum

- Wani sabon ango daga jihar Ibadan ya koka da halin da ya tsinci kanshi a sabon auren da ya yi

- Ya bayyana yadda sabuwar amaryarshi ta ke tsula mishi fitsarin kwance kowacce rana tun bayan aure

- Deji ya rasa yadda zai yi don a halin yanzu ya yi kaura daga gidansu don ya ce kaddara zata fada mishi

Kamar yadda Deji daga jihar Ibadan ya bayyana yadda amaryarshi ke yin amalala a kowacce rana. Ya fusata da lamarin kuma yana bukatar a raba auren. Ya ce hakan babbar masifa ce a al’adar magabatanshi.

A wata gajerar wasika da ya yi ga masani kuma mai bada shawara a harkar zamantakewa, Osigwe Omo-Ikirodah, Deji ya yi korafin cike da fushi. Ya bayyana yadda ya bar gidan kwata-kwata saboda wannan dabi’ar ta amaryarshi.

Ga abinda Deji ya ce a wasikarshi: “Fatan komai lafiya Osigwe. Ina cikin wata babbar matsala ne. Aurena duka-duka watanninshi uku kacal. Na auri wata yarinya ne daga Benin mai suna Adesuwa. Ba mu taba kwanciya ba har sai bayan aurenmu. Ina ganin saboda hakan ne bansan tana da wannan mummunar dabi’ar ba.

“Matata dai fitsarin kwance take yi kowacce rana. Ina tunanin ta san ba zan lamunci wannan mummunar dabi’ar bane shiyasa ta bukaci mu kauracewa juna kafin aurenmu.

“Daga yankin da nazo na jihar Ibadan, zama da ita babbar masifa ce. Na kai kara wajen mahaifina amma sai yace tsohon camfi ne na fitsarin kwancen. Akwai yuwuwar ta warke idan muka danganta da asibiti. Ya ce bai ga aibun hakan ba matukar tana da wasu halaye masu nagarta.

KU KARANTA: Babbar magana: Tilas ka aureni ko kuma na saka mazakutarka ta daina aiki - Cewar wata budurwa ga saurayinta

“Hakazalika, itama mahaifiyata haka tace. Abokai na kalilan da na sanar dasu halin da nake ciki suma haka suka ce.

“A gaskiya matata ma’aikaciyar jinya ce da ban taba ganin irinta ba. Koyaushe tana cikin farinciki kuma tana da wadatar zuci tare da hazaka. Kamar yadda muka yadda a yankinmu, duk macen da ke fitsarin kwance tana kawo rashin arziki ga duk makusancinta. Tunda na aureta, kwastomomina duk sun koma ‘yan bashi.

“Tunda na gane hakan, na tattara komatsaina na bar mata gidan. A halin yanzu matar abokina da nake gidanshi duk ranta ya baci. Ta bani wa’adin kwanaki biyu in sasanta da matata ko in bar gidan.

“A halin yanzu bansan abinda zanyi ba. Bansan kuma ko naje kotu za a amince da sakin ba. Me yakamata inyi?”

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel