Laifin kisan kai: Kotu ta yankewa dan wani babban basarake hukuncin kisa

Laifin kisan kai: Kotu ta yankewa dan wani babban basarake hukuncin kisa

Yarima Adewale Oyekan, dan marigayi Sarki Legas, Adeyinka Oyekan ya samu hukuncin kisa sakamakon kashe wata ‘yar kasuwa kuma ‘yar siyasa mai suna Sikirat Ekun da yayi.

Wata babbar kotu da ke Ikeja ce ta yankewa yariman mai shekaru 50 tare da hadiminsa mai shekaru 27 wannan hukuncin.

An fara sauraron shari’ar ne a ranar 14 ga watan Afirilu, 2015.

An gano cewa, yariman ya yi hayar hadiminsa Lateef Balogun a kan N6000 ne inda yasa shi ya kashe Ekun har lahira.

Wadanda aka yankewa hukuncin sun kasance a tsare tsawon shekaru 7. An gano cewa Balogun ya shake Ekun ne har lokacin da ta mutu sannan ya wurga gawarta a cikin wata rijiya mai zurfin kafa 1,000 a cikin gidanta.

DUBA WANNAN: Gwamnonin PDP biyu sun yi cacar baki a kan Buhari

Jastis Raliatu Adebiyi ta kamasu da laifin hada kai wajen cutarwa da kisan kai.

Ta ce: “Wannan shaidar a bayyane take kuma kwakkwara ce; kisan da ake zargin masu kare kansu da yi da gangan ne suka aikata hakan. Kotun ta gamsu da hujjojin da masu gurfanarwa suka bayyana a gabanta. An kamasu da laifuka biyu.”

Kotun ta gano cewa, wadanda aka gurfanar din sun aikata laifin ne a ranar 17 ga watan Oktoba, 2012 a gidan wacce ta rasun da ke lamba 5, titin Babatunde Lalega da ke Omole Phase One a jihar Legas. Masu gurafanarwar sun bayyana cewa, wacce aka kashe din tana aikin siyar da abinci ne. Kuma ta san Oyekan ne ta amintakar da ke tsakaninsa da mahaifiyarta.

An kuma gano cewa, bayan kashe Ekun, wadanda aka gurfanar din sun karbe kasuwancinta da dukiyoyinta.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Tags:
Online view pixel