Hukumar yaki da fasa kauri za ta dauki sabbin matasa 3,200 aiki

Hukumar yaki da fasa kauri za ta dauki sabbin matasa 3,200 aiki

Hukumar yaki da fasa kauri, kwastam ta sanar da aniyarta na fara daukan sabbin ma’aikata, inda za ta bude shafinta na yanar gizo don masu neman aikin su daura takardunsu, kamar yadda shugaban hukumar, Hamid Ali ya bayyana.

Jaridar Daily Trust ta ruwaito Hamid Ali, wanda ya samu wakilcin mataimakin shugaban kwastam, kuma babban jami’I mai kula da sashin cigaban ma’aikata, Sanusi Umar ya bayyana cewa hukumar za ta bude shafin ne daga 12 na daren Laraba, 18 ga watan Disamba.

KU KARANTA: Yansanda sun kama Sojan Najeriya da aikata halin bera a jahar Edo

Shugaban na kwastam yace hukumar za ta dauki tsawon makonni uku tana amsan takardun yan Najeriya masu sha’awar neman guraben aiki a cikinta, kamar yadda ya bayyana inda yace hukumar ta samu amincewar majalisar zartarwar Najeriya a kan batun.

Sai dai yace daga cikin ma’aikata 3,200 da za’a dauka, hukumar za ta dauki hafsoshin kwastam guda 800, sai kuma kananan jami’an kwastam guda 2,400 da suka hada da inspekta da sauran kurata.

Sa’annan Ali ya bayar da shafin yanar gizon da za’a bi wajen neman guraben aikin hukumar kwastam da cewa shi ne: www.vacancy.customs.gov.ng. “A shirye muke mu yi duk mai yiwuwa wajen tabbatar an gudanar da aiki na gaskiya da sahihanci ba tare da nuna son kai ko bambamci ba.”

Daga karshe shugaban na kwastam ya tabbatar da cewa babu ko sisi da za’a biya wajen neman guraben aiki a hukumar ta su, don haka yayi kira ga masu neman aiki su kiyayi duk wanda ya nemi su bashi kudi.

A wani labarin kuma, rundunar Yansandan Najeriya reshen jahar Edo sun kama wani jami’in rundunar Sojan Najeriya, Eyosu Kennedy mai shekau 25 da laifin tafka halin bera bayan ya saci wata mota kirar Toyota Camry.

Jami’in Sojan mai mukamin Private yana aiki ne a bataloiya ta 112 dake jahar Borno, kuma an gabatar da shi ga yan jaridu ne a sakatariyar Yansandan Najeriya dake garin Bini na jahar Edo.

Ku biyo mu a https://facebook.com/legitnghausa

ko a http://twitter.com/legitnghausa

KU LATSA: Hanyar sauko da sabuwar manhajar jaridar Legit.com Hausa cikin sauki

Ga masu shawara ko korafi, a same mu a labaranhausa@corp.legit.com

Sanarwa na musamman: Shafin NAIJ Hausa ya koma Legit Hausa

Source: Legit

Online view pixel