Kunne ya girmi kaka: Alakar sarautar 'Sarkin Bai' da jihadin Shehu bin Fodio

Kunne ya girmi kaka: Alakar sarautar 'Sarkin Bai' da jihadin Shehu bin Fodio

A ranar Lahadi ne sarkin sabuwar masarautar Bichi a jihar Kano, Aminu Ado Bayero, ya sauke 'Sarkin Bai' kuma hakimin Dambatta, Mukhtar Adnan, tare da maye gurbinsa da hakimin Makoda.

Dabo FM, wani gidan Radiyo mai zaman kansa a jihar Kano ya bayyana cewa an fara nada 'Sarkin Bai' a matsayin daya daga cikin masu nada sarki a Kano a shekarar 1954, kuma yana daga cikin wadanda suka nada sarkin Kano, marigayi Ado Bayero, a shekarar 1964.

A cikin wani littafi, "Jagora abun Koyi" - Alh. Mukhtar Adnan", da ya wallafa a shekarar 2003, marubuci Ado Ahmad Gidan Dabino, ya bayyana cewa ana samun sarautar " Sarkin Bai" ne daga kabilar Dambazawa, wadanda asalinsu Fulani ne daga kasar Senegal.

Dabo FM ta kara zakulo alakar da ke tsakanin Sarkin Bai da Shehu Usmanu bin Fodio.

DUBA WANNAN: Shugabannin kasashen Afrika 7 da suka mallaki manyan kudade

Kimanin karni biyu da suka wuce ne Dambazawa suka shigo yankin jihar Borno inda daga nan suka shiga garin Danbam a jihar Bauchi, daga bisani kuma suka shiga yankin gabashin jihar Kano inda suka kafa garin Dambazau da ke yankin karamar hukumar Takai a yanzu.

Dambazawa sun cigaba da yaduwa zuwa cikin garin Kano inda har a shekarar 1806, bayan jihadin Dan Fodio, suka karbe iko da yankin gidan Sarkin Bai da ke kusa da kasuwar Jakara a birnin Kano.

Modibbo, shugaban kabilar Dambazawa na wancan lokacin, ya kasance dalibi ga Dan Fodio wanda bayan dawowarsa gida ya tattara mutanen kabilar tare da saka su yin mubaya'a ga Shehu tun kafin yakin Shehu da Sarkin Gobir.

Kabilar Dambazawa ta Sarkin Bai ta tara wa Dan Fodio dukkan dakarunta na yaki a arewacin masarautar Kano a Dambatta tun kafin Shehu ya iso Kano a yi gumurzu da shi.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit

Online view pixel