Labarin Adamu Garba: Dan Fulanin daya fara aiki a Maigadi a jami’a, har ya zama Malami

Labarin Adamu Garba: Dan Fulanin daya fara aiki a Maigadi a jami’a, har ya zama Malami

Haka abin yake, duk wanda yasa hubbasa kuma ya rike gaskiya, sai Allah Ya shiga lamarinsa, kuma Ya taimakeshi. Wannan shi ne labarin wani bafulatani a jahar Taraba, Adamu Garba, kamar yadda shafin Northeast Reporters na kafar Facebook ta bayyana.

Majiyar Legit.ng ta ruwaito Adamu Garba matashin bahillace ne daya rungumi aikin kiwon dabbobi kamar dai yadda yawancin Fulani suke yi, daga bisani bayan an bude jami’ar gwamnatin tarayya a garin Wukari sai ya samu aiki a jami’ar a matsayin maigadi.

KU KARANTA: Kalaman Aisha Buhari sun tabbatar da Buhari cikakken dan siyasa ne – Yahaya Bello

Labarin Adamu Garba: Dan Fulanin daya fara aiki a Maigadi a jami’a, har ya zama Malami
Adamu Garba
Asali: Facebook

Sai dai ashe koda Adamu yake aikin kiwon, tuni ya yi karatu a kwalejin ilimi inda ya mallaki shaidar kammala karatu ta NCE, don haka bayan ya fara aiki a jami’ar Wukari a shekarar 2012, daga bisani sai ye nemi gurbin cigaba a karatu a jami’ar.

Haka kuma aka yi, Adamu danfulani ya samu gurbin karatu a jami’ar, ya yi karatunsa ya kammala a farkon shekarar nan, kuma ya kammala da shaidar digiri mai daraja ta 2, watau 2:1, a yanzu dai maganan da ake yi jami’ar ta dauke shi aiki a matsayin Malami dake taimaka ma manyan Malamai.

Labarin Adamu Garba: Dan Fulanin daya fara aiki a Maigadi a jami’a, har ya zama Malami
Adamu
Asali: Facebook

A wani labarin kuma, babban Alkalin Alkalan Najeriya, mai sharia Ibrahim Tanko Muhammad ya nemi a gudanar da gyaran fuska ga kundin tsarin mulkin Najeriya ta yadda zai kunshi tanade tanaden shari’ar Musulunci a cikinsa.

Alkali Ibrahim ya bayyana haka ne yayin da yake bude taron Alkalan Najeriya karo na 20 dake gudana a tsangayar ilimin sharia na jami’ar Ahmadu Bello, inda ya yi jawabi a kan ‘Adana bayanan kwangila a mahangar shariar Musulunci: Yadda ake yi, ya aka yi shi a baya’.

Cibiyar ilimin shariar Musulunci ta jami’ar ABU tare da hadin gwiwar cibiyar sharia ta kasa ne suka shirya taron, inda Alkalin Alkalai ya yi kira ga malamai dake koyar da ilimin sharia su dauki gabaran ganin an sauya yadda ake koyar da ilimin shariar Musulunci.

Ku biyo mu a https://facebook.com/legitnghausa

ko a http://twitter.com/legitnghausa

KU LATSA: Hanyar sauko da sabuwar manhajar jaridar Legit.com Hausa cikin sauki

Ga masu shawara ko korafi, a same mu a labaranhausa@corp.legit.com

Sanarwa na musamman: Shafin NAIJ Hausa ya koma Legit Hausa

Asali: Legit.ng

Authors:
Mudathir Ishaq avatar

Mudathir Ishaq Mudathir Ishaq is the head of the Hausa desk at Legit.ng. He studied Industrial Chemistry as first degree at the University of Abuja, Journalism (CSR Specialization) with the Michigan State University and runs MSc Industrial Chemistry from the Nasarawa State University, Keffi. With more than a decade experience in news reporting and content editing, he has interviewed influential personalities. He can be reached on: mudathir.ishaq@corp.legit.ng