ICPC na neman wani dan Majalisar Tarayya ruwa a jallo

ICPC na neman wani dan Majalisar Tarayya ruwa a jallo

Hukumar yaki da rashawa ta ICPC ta bayyana neman dan majalisa mai wakiltar Maiyama/Koko/Basse a majalisar tarayya, ido ruwa jallo. Hukumar na neman Shehu Koko-Mohammed ne bayan da ya ki bayyana gaban hukumar.

A takardar da hukumar ta fita a ranar Alhamis, Daraktan ICPC, Rasheedat Okoduwa, ta ce matakin da suka dauka ya zama dole saboda binciken da suke yi a kanshi.

Kamar yadda takardar tace: Wanda hotonsa ke wallafe a nan shine Shehu Koko Mohammed. Hukumar ICPC na nemansa ido ruwa jallo sakamakon rashin bayyana da yayi a gaban hukumar, bayan da ta bukaci hakan.

DUBA WANNAN: Kotu ta kwace rawanin wani babban basarake, ta bukaci a maye gurbinsa da gaggawa

Honarabul Mohammed dan asalin jihar Kebbi ne kuma yana wakiltar mazabar Maiyama/Koko/Basse a matakin tarayya. An haifeshi a ranar 16 ga watan Yuni 1978, kuma yana da duhun fata. Yana zama ne a Ofishin kamfen na Wamban Koko, titin Jega, Maiyama, jihar Kebbi.

Duk wanda ya samu wani bayani mai muhimmanci a kan inda yake, ya kai rahoto ga hedkwatar ICPC a Abuja ko wani ofishinsu mafi kusa ko kuma ofishin ‘yan sanda. Za a iya kiran lambobin waya kamar haka: 0803-123-0280, 0803-123-0281, 0803-123-0282, 0705-699-0190, 0705-699-0191 ko ka kira (0800-2255-4272)

Rasheedat A. Okoduwa, mni

Daraktan wayar da kan jama’a

A madadin: Shugaban hukumar

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit

Online view pixel