Abuja: Dan acaba ya caka wa jami'in hukuma mai suna Danlami Ibrahim wuka a kirji

Abuja: Dan acaba ya caka wa jami'in hukuma mai suna Danlami Ibrahim wuka a kirji

An samu rudani ranar Alhamis a Abuja bayan wani dan achaba ya caka wa Danladi Ibrahim, mamba a rundunar jami'an kiyaye hadurra ta Abuja, wuka.

SaharaReporters ta rawaito cewa jami'in yana aiki ne da ayarin jami'an da aka tura yankin Apo a unguwar Gudu, inda aka haramta acaba.

Lamarin ya faru ne yayin da jami'an tawagar suka dira unguwar tare da kwace baburan 'yan acaba, lamarin da ya fusata masu sana'ar acaban har suka far wa tawagar jami'an domin krbar baburansu.

A cewar SaharaReporters, a yayin da ake cacar baki a tsakanin jami'an da fusatattun 'yan acabar ne sai day dg cikinsu ya fitar da wuka ya caka wa Ibrahim kirji.

Jaridar ta kara da cewa dan acabar da ya caka wa jami'in wuka ya gudu da babur dinsa, sannan daga baya sauran 'yan acabar ma suka zare jiki suka gudu.

Duk da an garzaya da jami'in zuwa asibiti domin ceton ransa, SaharaReporters ta rawaito cewa yana cikin mawuyacin hali saboda zurfin da zurfin sukar da dan achabar ya yi masa.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Authors:
Mudathir Ishaq avatar

Mudathir Ishaq Mudathir Ishaq is the head of the Hausa desk at Legit.ng. He studied Industrial Chemistry as first degree at the University of Abuja, Journalism (CSR Specialization) with the Michigan State University and runs MSc Industrial Chemistry from the Nasarawa State University, Keffi. With more than a decade experience in news reporting and content editing, he has interviewed influential personalities. He can be reached on: mudathir.ishaq@corp.legit.ng