Farfesan Lissafi da ya dauki niyyar karyata Qur'ani ya zama Musulmi

Farfesan Lissafi da ya dauki niyyar karyata Qur'ani ya zama Musulmi

A shekarar 1977 ne Gary Miller, farfesan Lissafi a jami'ar Toronto da ke kasar Canada, ya dauki aniyar karanta Qur'ani domin gano kura - kuran dake cikinsa don nuna wa Musulman duniya cewa ba a kan hanyar gaskiya suke ba.

Farfesa Miller, mai tsaurin akidar addinin Kirista, ya dauki wannan niyya ne bayan ya lura cewa yana wahala Musulmi ya canja addini zuwa Kirista.

Abu na farko da farfesa Miller ya ce ya ci karo da shi a cikin Qur'ani, ba sau daya ba, shine kalubantar jama'a da aka a kan su yi amfani da hujja.

"Shin ba zasu kasance masu kokonto a kan Qur'ani ba? da a ce wani ya saukar da Qur'ani ba Allah ba, to tabbas za a samu rudar wa a tattare da shi." (Qur'an 4:82).

"...idan kuma kun kasance masu a cikin masu kokonto a kan sakon da muko aiko shi Annabi Muhammad), ku gwada samar da wata Surah kamar wannan, sannan sai ku kwatanta." (Quran 2:23)

Bayan ya shafe lokaci mai tsawo yana nazarin Qur'ani, farfesa Miller ya gamsu cewa maganganun dake cikin Qur'an su fi karfin a ce aikin mutum ne, a saboda haka ya karbi addinin Islama tare d cigaba da yin kira ga jama'a a kan su dawo hanyar gaskiya.

Farfesan Lissafi da ya dauki niyyar karyata Qur'ani ya zama Musulmi

Farfesa Gary Miller
Source: Twitter

Tun daga nan farfesa Miller ya fara shirya lacka domin sanar da jama'a irin dumbin ilimin da ya ci karo da shi yayin da yake nazarin Qur'ani da niyyyar gano kura - kuran da ke cikin domin jan hankalin Musulmai su koma Kiristoci.

Manyan malaman addinin Islama a fadin duniya sun nuna matukar mamakinsu a kan yadda mutum mai akidar Kiristanci da zurfin ilimin boko ya koma Musulmi. Sun alakanta hakan da zallar gaskiya da ya ci karo da ita yayin da yake nazarin Qur'ani.

Kazalika, sun mika godiya ga ubangiji da ya nuna masa gaskiya kuma ya bashi ikon karbar ta hannu biyu da kuma zuciya daya.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit

Online view pixel