Garba Shehu fuska biyu gareshi, saboda haka lokaci yayi da zai ajiye aikinsa - Aisha Buhari

Garba Shehu fuska biyu gareshi, saboda haka lokaci yayi da zai ajiye aikinsa - Aisha Buhari

- Uwargidan shugaban kasa Muhammadu Buhari, ta ce ya kamata hadimin shugaban kasa ya ajiye aikinshi

- Ta bayyana cewa, Garba Shehu fuska biyu gareshi don kuwa yana yi wa miyagu aiki ta kasan kasa

- Ta kara da cewa, ita da iyalanta basu amincewa dashi yanzu, don kuwa ba ya kare mutuncinsu

Uwargidan shugaban kasa Muhammadu Buhari, Aisha ta ce ya kamata hadimin shugaban kasa Buhari ya ajiye mukaminshi saboda gazawa wajen gudanar da aikinshi.

A wani sako da ta wallafa, Aisha ta nuna takaici bisa yadda ta ce Garba Shehu ke kware wa Buhari baya, kasancewarshi yaron wasu miyagu.

Ta kara da koka wa bisa yadda wani lokaci a kan samu abin magana da ke shafar ta ko kuma Shugaba Muhammadu Buhari, amma Garba Shehu ba ya tsawatarwa ko ya kare martabarsu.

KU KARANTA: Mijin aure nake nema ruwa a jallo - Rayya ta shirin 'Kwana Casa'in'

Da take cewa ba zata lamunci hallayar Garba Shehu ba, Aisha Buhari ta ce ya taba cewa ba zai bari ofishinta ya yi aiki ba. Kuma ya shaida wa hadimansa cewa Mamman Daura ne ya sa shi fadin hakan.

A cewarta, fuska biyu Garba Shehu yake yi da irin zubewar mutuncin da ya jawo wa fada da iyalan shugaban kasar. Ta kara da cewa, ita da iyalanta a yanzu basu aminta dashi ba. Kawai kamata ya yi Garba Shehu ya ajiye aikinsa.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit

Online view pixel