Yan Najeriya 4 sun shiga hannu a kasar Amuka kan satar naira biliyan 6.5
Gwamnatin kasar Amurka ta sanar da kama wasu yan Najeriya guda hudu da laifin satar dala miliyan 18, kimanin naira biliyan 6 (N6,507,000,000) ta amfani da yanar gizo, a ranar Talata, 10 ga watan Disamba.
Jaridar Guardian ta ruwaito sashin shari’a na gwamnatin kasar Amurka ce ta sanar da kama yan Najeriya, inda tace sun saci kudaden ne a hada hada 100 da suka yi a asusun bankuna daban daban.
KU KARANTA: Ramin karya kurarre ne: Yar uwar Abdulrashid ta tona masa asiri a gaban Alkali
Majiyar Legit.ng ta ruwaito sunayen yan Najeriya kamar haka; Oladayo Oladoku, Farouk Kukoyi, Baldwin Osuji da Henry Ogbuokiri, sa’annan tace akwai sauran abokan aikinsu 11 da suke tafka wannan ta’asa tare wanda a yanzu haka sun ranta ana kare.
“Kamar yadda aka kawo mana kara, wadannan mutane 15 suna amfani da bankuna ne wajen satar kudi, a haka suka sace dala miliyan 18.” Inji shugaban Yansandan Homeland, Peter C. Fitzhugh.
Mista Peter yace za su cigaba da aiki tukuru don tabbatar da sun gudanar da cikakken bincike a kan wadannan miyagu wanda suke cutar da mutanen kasar Amurka, sa’annan ya yi alkawarin hukumomin kasar Amurka za su yi aiki tare don tabbatar da nagartar tsarin cinikayyar kudade na kasar Amurka.
A yanzu dai mutanen nan suna fuskantar hukuncin daurin shekaru talatin talatin a gidan yari idan har kotu ta kamasu da laifi.
Ma’aikatar sharian ta ce miyagun sun bude asusun bankuna guda 60 ta hanyar amfani da takardun wasu mutane na daban ba tare da sun sani ba, daga nan sai su yo damfara, sai su tura kudaden da suka damfaro zuwa cikin asusun da suka bude da sunayen mutanen, sai kuma su kwashe kudin zuwa nasu asusun bankin ko kuma su cire kudin da kansu.
A wani labarin kuma, yar uwar Abdulrashid Maina da ake tuhuma da satar fiye da naira biliyan 2 a hukumar fansho ta kwance masa zani a kasuwa, inda ta nesanta kanta daga kamfanoni da asusun banki da Maina ya bude da sunanta yana hada hadar makudan kudade, ba tare da saninta ba.
Ku biyo mu a https://facebook.com/legitnghausa
ko a http://twitter.com/legitnghausa
KU LATSA: Hanyar sauko da sabuwar manhajar jaridar Legit.com Hausa cikin sauki
Ga masu shawara ko korafi, a same mu a labaranhausa@corp.legit.com
Sanarwa na musamman: Shafin NAIJ Hausa ya koma Legit Hausa
Asali: Legit.ng