Wa'iyazubillah: An yankewa wani mutumi hukuncin kisa bayan yaje an sauya masa kama irin ta Annabi

Wa'iyazubillah: An yankewa wani mutumi hukuncin kisa bayan yaje an sauya masa kama irin ta Annabi

- Hukumar shari’ar musulunci ta kasar Saudi Arabia ta yankewa wani matashi hukuncin kisa tare da bulala 200

- Hukumar ta kama saurayin da laifin yin aiki har kashi 23 don komawa kamannin Annabi Muhammad

- Kamar yadda shari’ar musuluncin ta bayyana, hakan tozarci ne da shirka, laifuka biyu da suke da hukuncin kisa

Abdulaziz Sudairi matashi ne mai shekaru 23 a duniya kuma mazaunin gwarin Najran ne kusa da iyakar Yemeni. An yanke wa matashin hukuncin bulala 200 kafin a tsinke kanshi da takobi.

Matashin sananne ne a shafin Instagram. Ya kai ziyara Isra’ila sau da yawa a cikin shekaru biyu da suka gabata inda aka yi mishi aiki kashi 23 a fuskarshi don ya koma kamannin Annabi Muhammad.

Ya samu matsaloli da dama daga hukumomin kasar Saudi Arabia, amma wata wallafa da ya yi a shafinsa na Instagram ya jawo mishi babban matsala. A watan Yuni ne kuma kwamitin habaka tarbiya mai nagarta da hana tashin-tashina ta ‘yan sandan musulunci suka yi mishi caa.

Sudairi ya walllafa hotonshi bayan an yi mishi aikin inda ya kara da cewa, “Aiki biyu ko uku kacal suka rage, zan zama koma kamannin Muhammad. Da izinin Allah.”

An cafke shi kuwa bayan kwanaki uku kacal inda aka wurga shi gidan yari tare da tambayoyi masu tarin yawa, kafin a gurfanar dashi a gaban kuliya.

KU KARANTA: Kura ta kai bango: Zamu fara zanga-zanga idan har bamu samu mazajen aure ba cikin shekarar nan - Kungiyar likitoci mata

Kamar yadda hukuncin kotun musuluncin ya bayyana, yunkurin komawa kamannin Annabi da Sudairi yayi, ya zamo batanci da shirka, laifukan kuwa da suka dau hukuncin kisa a shari’ar musulunci.

“Ba musulunci bane ka yi kamanceceniya da Annabi. Cin zarafi ne ga Annabin da kuma musulunci. Wannan mummunan zunubin ya cancanci hukunci.” Inji hukuncin

Sanannen abu ne cewa, yanayin tsarin shari’ar Saudi Arabia mai tsauri ce. Ta kunshi manyan hukunce-hukunce da hanyoyin aiwatar dasu kala-kala.

Daga cikin hukuncin shari’ar akwai bulala, cire hannu ko kuma kisa ta hanyar fille kai da takobi, jefewa ko kuma kisa ta hanyar rataya.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit.ng

Online view pixel