An dauki mutumin da tusar shi ke kashe sauro aiki a wani kamfanin kashe kwari

An dauki mutumin da tusar shi ke kashe sauro aiki a wani kamfanin kashe kwari

- Joe Rwamirana mutum ne mai shekaru 48 a duniya dan kasar Uganda amma mazaunin Kampala

- Ya fara samun miliyoyin kudi ne bayan da kamfanoni da dama suka daukeshi aiki

- Kamfanonin na yin amfani da tusarshi ne a matsayin sinadarin sarrafa maganin kwari

Joe Rwamirana wani mutum ne dake zama a Kampala amma dan asalin kasar Uganda ne. Mutumin mai shekaru 48 ya fara samun miliyouin kudade ne bayan da kamfanonin maganin kwari suka gane tusarshi tana hallaka sauro da wuri.

A yanzu dai, wasu daga cikin kamfanonin maganin sauro a kasar, suna biyan Joe domin nazari a kan nau'in tusarshi tare da mayar da ita sinadarin hada maganin kwari.

Jaridar Talk ta ruwaito cewa, Tusar Joe tana kashe dukkanin wani kwaro da yake kusa da shi na tsawo mita 6.

Hakazalika, ta tabbatar da cewa, tusar tana kashe kwari masu tashi wadanda basu fi girman sauro ba.

Jaridar Independent Najeriya ba a barta a baya ba. Ta shaida cewar, tun lokacin da Joe yake karamin yaro, ya kasance garkuwa ga mutanen gari, musamman manyan kauyensu. Su kan kaishi gidajensu a duk lokacin da cutar cizon sauro ta barke, don ya zama kariya garesu.

Ta kara da cewa, duk wanda yake kwana da Joe, bai taba kamuwa da ciwon Malaria ba. Hakazalika, Joe bai san meye cizon sauro ba.

Gidan rediyon Dabo FM ya binciko mutumin inda ya yi karin haske game da batun. Ya bayyana cewa: "Ina cin abinci kamar kowa amma babu wani kwaro da yake iya hawa jikina ko da kuwa mai tashi ne.

"Ina wanka kullum, kuma Tusa ta irin ta kowa ce. Sai dai tawa tusar tana kashe kwari, musamman sauro."

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit.ng News

Online view pixel