Aiyukan alherin marigayi Sani Abacha da kwata - kwata ba a maganarsu

Aiyukan alherin marigayi Sani Abacha da kwata - kwata ba a maganarsu

Shakka babu marigayi janar Sani Abacha yana daga cikin tsofin shugabannin Najeriya da ke shan zagi, wasu na alakanta hakan da cewa don ba ya raye ne.

Ba kasafai ake jin 'yan Najeriya suna tattauna wa a kan alheran da marigayi Abacha ya yi ba lokacin da yake kan mulki ko kuma fadar wasu halayensu na kirki, masu nagarta, a matsayin shugaba ba.

Marigayi Abacha mutum ne mai tarbiya da matukar lissafi tare da daukan matakan da zasu inganta rayuwar 'yan Najeriya da kuma daga daraja da kimar Najeriya a nahiyar Afrika, kamar yadda fitacciyar marubuciya, Chimamanda Ngozi Adichie, ta bayyana yayin wata hira da ita a wata kafar wa ta duniya (Ted Talk).

Ga wasu daga cikin alherai da halaye nagari da Abacha keda su, wadanda kuma kwata - kwata ba a maganarsu yanzu;

1. Lissafi da tsaya wa bisa tafarkin gaskiya: Marigayi Abacha ya rike mukamai da dama a rundunar soji kafin daga bisani ya zama shugaban kasa. Abokansa na aiki, da suka hada da na gaba da na baya da shi, sun bayar da shaidar cewa marigayi Abacha yana da hannu a juyin mulkin soji tun yana rike da mukamin Laftanal (2nd Lieutant) saboda kaifin basirarsa da kuma iya lisssafa al'amura kafin a aiwatar da su.

Sun bayyana cewa marigayi Abacha ba ya shakkar tsara juyin mulki ga shugaban kasar da ya taimaka wa ya hau mulki matukar ya gamsu cewa ya bar tafarkin tsari da sharudan da suka zama sanadin hawansa kujerar shugaban kasa.

DUBA WANNAN: Tinubu ya gana da Atiku da gwamna Fintiri

2. Tsantseni da kokarin bayyana kudaden da ake kashe wa a gwamnatance: Marigayi Abacha ya taba umartar hukumar sarrafa rarar kudin man fetur (PTF) da take wallafa asusunta domin kowa yake ganin adadin kudin da suke kashe wa.

Ashekarar 1997, asusun PTF ya nuna cewa ta kashe biliyan N24.3bn domin gina hanyoyi, biliyan N21.2 a bangaren tsaro, biliyan N7.8 a bangaren lafiya da kuma biliyan N3 a kan wasu sauran aiyuka.

3. Tsaro: Babbar nasarar da Abacha ya samu a mulkinsa shine tabbatar da tsaro. Marigayi Abacha ya yi amfani da gogewarsa a matsayinsa na soja wajen yakar aiyuka da kungiyoyin 'yan ta'adda.

4. Kafa hukumar PTF domin inganta bangaren ilimi, lafiya da sauransu:

Marigayi Abacha ne ya kafa PTF domin tabbatar da cewa dukkan 'yan Najeriya sun ci moriyar ribar da kasa ke samu daga sayar da danyen man fetur.

PTF, a karkashin jagorancin janar Muhammadu Buhari, ta gina hanyoyi a kudu da arewacin Najeriya tare da bayar da tallafin kayan karatu ga makarantu.

5. Rawar da Najeriya ta taka wajen tabbatar da samun zaman lafiya a Afrika: An samu yawaitar rigingimu a kasashen Afrika a tsakanin 1993 zuwa 1998, lamarin da yasa Abacha ya bawa kungiyar kasashen nahiyar Afrika (ECOWAS) tallafin bataliyar rundunar sojoji daga Najeriya domin a tura su zuwa kasashen dake fama matsalolin tsaro.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel