Jam’iyyar APC ta yi ‘Cinye du’ a zaben kananan hukumomin jahar Ekiti, PDP ta koka

Jam’iyyar APC ta yi ‘Cinye du’ a zaben kananan hukumomin jahar Ekiti, PDP ta koka

Hukumar zabe mai zaman kanta ta jahar Ekiti, EKSIEC, ta sanar da yan takarar jam’iyyar APC a matsayin wadanda suka lashe zaben shuwagabannin kafatanin kananan hukumomin jahar guda 16 da aka gudanar a ranar asabar.

Kamfanin dillancin labarun Najeriya, NAN, ta ruwaito cewa EKSIEC ta sanar da sakamakon zaben ne a ranar Lahadi, 8 ga watan Disamba, sai dai hukumar bata sanar da sakamakon zaben kansiloli 177 dake kananan hukumomin ba.

KU KARANTA: Jerin ‘Ya ‘yan Shugaba Buhari da Makarantun da su ka yi karatu

Shugaban hukumar, mai sharia Jide Aladejana ne ya sanar da sakamakon a Ado Ekiti, babban birnin jahar Ekiti, inda ya tabbatar da cewa babu wanda ya rasa ransa a yayin zaben, ba kamar yadda kafafen watsa labaru suke ruwaitowa ba.

“Babu wanda aka kashe a rumfar zabe na 006 dake mazaba ta 7 a Ikere a ranar Asabar, babu wanda aka harba, amma dai mun samu rahoton wani ya zo da rikici ya kwashe takardun zaben da ba’a yi amfani dasu ba. A gaba daya rumfar zaben, masu zabe 280 ne kawai, don haka babu ta yadda lamarin zai shafi sakamakon zaben.” Inji shi.

Jide ya bayyana a gudanar da zaben cikin zaman lafiya, inda ya yaba ma hukumomin tsaro dake jahar bisa rawar da suka taka wajen tabbatar da babu wanda aka yi ma barazana wajen kada kuri’arsa.

Sai dai, duk da cewa jam’iyyar PDP ta fafata a zaben tare da sauran jam’iyyu guda 13, amma a yanzu ta koka kan sakamakon zaben, inda tace bata amince da sakamakon ba saboda a cewarta shiri ne kawai.

Shugaban jam’iyyar PDP na jahar Ekiti, Cig Gboyega Oguntuase ne ya bayyana haka, inda yace akwai yiwuwar su garzaya gaban kotu: “Bayanan da muka samu sun tabbatar da an yi rikici a wurare da dama a ranar zaben, musamman a Ikere, inda aka kashe mutum 1, da jikkata mutane 4.”

Ku biyo mu a https://facebook.com/legitnghausa

ko a http://twitter.com/legitnghausa

KU LATSA: Hanyar sauko da sabuwar manhajar jaridar Legit.com Hausa cikin sauki

Ga masu shawara ko korafi, a same mu a labaranhausa@corp.legit.com

Sanarwa na musamman: Shafin NAIJ Hausa ya koma Legit Hausa

Source: Legit.ng

Online view pixel