Jerin ‘Ya ‘yan Shugaba Buhari da Makarantun da su ka yi karatu

Jerin ‘Ya ‘yan Shugaba Buhari da Makarantun da su ka yi karatu

A ‘yan kwanakin nan ne Aisha Buhari II ta kammala karatun Digirinta a kasar Ingila. Aisha, ta gama karatu ne ta na da shekaru 21 daga wata Jami’ar da ke yankin Greenwich a birnin Landan.

Mun kawo jerin makarantun da ‘Ya ‘yan shugaban kasar su ka yi karatu kamar yadda Jaridar Premium Times ta tsakuro daga littafin da Farfesa John Paden ya rubuta a kan ‘ya ‘yan shugaban.

1. Fatima

Fatima Buhari ta fara karatun Firamare ne a Makarantar Sojojin sama da ke Legas. Daga nan ta tafi Kwalejin gwamnati ta Kaduna. Sannan kuma ta halarci jami’ar Ahmadu Bello da ke Zariya. Fatima ta yi Digirgir a makarantar koyon kasuwanci ta jami’ar Stratford da ke kasar Ingila.

2. Hadiza

Nana-Hadiza ta halarci makarantar nan ta Essence International School da Jami’ar Kent da ke kasar Ingila. Hadiza ta yi Digirgir ne a Jami’ar Buckingham, kafin ta kara yin wani a fannin harkokin kasashen waje a Najeriya. Diyar shugaban kasar ta kuma yi karatu a NTI da Kad Poly.

3. Safinatu

Safinatu ta halarci Essence International School da ke Kaduna tare da ‘Yar uwarta. Haka zalika ta yi Digiri a jami’ar Kent ta Birtaniya. Ta kara yin wasu Digirin a jami’o’in Plymouth da Ardent a UK.

4. Halima

Halima Buhari ta yi Sakandare a International School, Kaduna. Sannan ta garzaya Makarantar Birtaniya da ke babban birnin Togo. Daga nan Halima ta tafi Makarantar Bellerby ta Brighton. Halima ta yi Digirinta a Jami’ar Leiciester, sannan ta zarce makarantar koyon aikin shari’a.

KU KARANTA: Gwamnati ta sa baki bayan Tsageru sun nemi su ga bayan Minista a kasar waje

5. Yusuf

Shi ma Yusuf Buhari ya yi karatu a Kaduna International School da Makarantar Turawan da ke Lome. Ya halarci kwalejin Bellerby a Ingila, kafin ya yi Digirinsa a Jami’ar Surrey ta kasar wajen.

6. Fatima

Zahra Buhari ta yi Firamare da Sakandare a gida Daga nan ta tafi Makarantar Bellerby a kasar Ingila. Bayan ta kammala ta samu shiga jami’ar Surrey ta karanci ilmin kimiyyar kananan halittu.

7. Aisha

Aisha Buhari (karama) ta bi sahun ‘Yan uwanta a Kaduna International School. Daga nan sai ta tafi Jami’ar Ravensbourne da ke Landan inda ta fita da matakin farko a bangaren daukar hoto.

8. Amina

Amina Buhari wanda ita ce ‘yar autar shugaban kasa, ta soma karatunta a Kaduna International School kafin shugaba Muhammadu Buhari ya tattara ya koma fadar shugaban kasa a Abuja.

Mai dakin shugaban kasar watau Hajiya Aisha Buhari ta yi Digiri a bangaren gudanar da mulki daga Jami’ar Ambrose Ali, daga baya ta yi Digirinta na biyu a harkokin kasar waje a NDA.

Har ila yau, Uwargidar shugaban kasar ta samu shaidar Difloma daga Makarantar koyon harkar kwalliya ta Carlton da ke Garin Windsor a kasar UK. Ta kuma yi PGD a wannan fanni a Faransa.

‘Ya ‘ya 2 da ba a ambata ba, Zulaihat-Junaidu Buhari da Musa Buhari sun rasu ne a shekarun baya.

Idan ku na da wata shawara ko bukatar bamu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewa tare da mu.

Ga masu bukatar manhajar mu na Musulunci sai a bibiyi wannan shafi

https://fb.gg/play/ramadan_ramadan

Asali: Legit.ng

Tags:
Online view pixel