Jihohin Najeriya uku da suka ciri tuta a 'cin hanci' a shekarar 2019 - Kididdigar NBS

Jihohin Najeriya uku da suka ciri tuta a 'cin hanci' a shekarar 2019 - Kididdigar NBS

Wani sabon rahoton bincike da hukumar kididdiga ta kasa (NBS) ta fitar a cikin mako ya nuna cewa har yanzu rundunar 'yan sanda ce a kan gaba idan ana maganar hukumomi ko ma'aikatun gwamnati da cin hanci ya yi wa katutu.

Hukumar NBS ta saki sakamakon rahoton binciken mai lakabin 'bincike na biyu a kan cin hanci a Najeriya' ranar Juma'a.

A cikin rahoton, hukumar NBS ta ce ta gudanar da binciketa ne tare da hadin gwuiwar ofishin yaki da laifuka da miyagun kwayoyi na majalisar dinkin duniya da sauran wasu kungiyoyi da hukumomi na kasa da kasa.

Mista Yemi Adeleran, wakilin shugaban hukumar NBS, Dakta Yemi Kale, shine wanda ya gabatar da sakamakon rahoton binciken a dakin taro (conference Centre) da ke Abuja.

Bayan gabatar da alkaluman cin hanci a ma'aikatu da hukumomin gwamnati, rahoton ya nuna jihohin da suke kan gaba a bangaren cin hanci da rashawa.

Jihar Kogi ce ta fi kowacce jiha fama da matsalar cin hanci da rashawa da kaso 45%, sai jihar Gombe da kaso 45%, jihar Ribas ce a mataki na uku da kaso 43, sai kuma jihar Adamawa a mataki na hudu d kaso 41%.

DUBA WANNAN: Dan sanda ya harbe wani matashi da ya rama marin da ya sharara masa

Imo ce jihar dake da karancin matsalar cin hanci da kaso 17.6%, jihohin Jigawa, Kano da Filato sune ke biye da jihar Imo.

A mataki na shiyya, NBS ta ce yankin arewa ta tsakiya ne ya fi fama da matsalar cin hanci, yayin da yankin arewa maso yamma shine yankin dake da karancin matsalar cin hanci.

NBS ta ce ta samo alkalumanta ne daga hannun 'yan Najeriya, kuma a cikin Najeriya.

A shekarar 2016 ne hukumar NBS ta gudanar da kididdiga a kan cin hanci a tsakanin ma'aikatu da hukumomin gwamnati, inda ta bayyana cewa rundunar 'yan sandan Najeriya ce a kan gaba idan batun cin hanci da rashawa ake yi a kasa.

A sabon rahotonta na shekarar 2019, shekaru uku bayan rahoton farko, har yanzu rundunar 'yan sanda ce a sama a jerin hukumomin da cin hanci ya samu gurbin zama duk da ta sauko kaso zuwa kaso 33% daga kaso 46% a shekarar 2016.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel