Shugaba Buhari ya taya shagon dan dambe, Anthony Joshua, murna

Shugaba Buhari ya taya shagon dan dambe, Anthony Joshua, murna

Shugaba Muhammadu Buhari ya taya shagon duniya, Anthony Joshua, murnan nasara a damben da ya gudana a daren Asabar tare da dan kasar Mexico, Andy Ruiz.

Shugaba Buhari ya jinjinawa Anthony Joshua kan kawo farin ciki ga miliyoyin yan Najeriya dake gida da kasashen waje da sukayi tsayin daka wajen ganin cewa za kwato bel-bel din da ya rasa watanni shida da suka gabata.

Buhari yace: "Faduwar namiji ba karshen rayuwarsa bane. Kowace rana zai iya farfadowa. Wannan darasi ne da ya kamata mu dauka daga gareka a matsayin kasa."

DUBA NAN Yadda AbdulAziz Yari ya biya kansa N350m ana saura kwana biyu ya sauka mulki

Mun kawo muku rahoton cewa Anthony Joshua ya karbe kambunsa na babban wasan dambe a wata gagarumar karawa da ya yi a Saudi Arabiya inda ya nunawa Andy Ruiz Jr bajintarsa wannan karo a duka zagayen 12.

‘Dan wasa Anthony Joshua ya samu ramuwar gayyar da ya ke nema tun a lokacin da Andy Ruiz ya doke sa a Birnin New York a farkon bana. Wannan karo Joshua ya nunawa Ruiz da sauransa.

Bayan wannan nasara, Joshua ya samu kambu 2, daidai da Muhammad Ali, Mike Tyson da Lennox Lewis. An yi wannan wasa ne a kasar Sahara a Diriyah, a wani fili mai cin mutum 15, 000.

Anthony Joshua ya fito da shirinsa. A zagaye na takwas, Ruiz ya nemi ya yi wa Joshua irin dukan da ya taba yi masa. ‘Dan wasan bai karaya ba, inda a zagayen karshe ya koyawa Ruiz Jr. hankali.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit.ng News

Tags:
Online view pixel