Babbar magana: Allah yayi mini baki babu wanda ya isa ya hanani magana - Aisha Buhari

Babbar magana: Allah yayi mini baki babu wanda ya isa ya hanani magana - Aisha Buhari

- Uwargidan shugaban kasa Muhammadu Buhari ta bayyana cewa, babu abinda zai hanata magana a kan kalubalen da kasar nan ke fuskanta

- Ta bayyana cewa, yancin magana hakki ne na kowanne dan kasa kamar yadda kundin tsarin mulkin kasar nan ya tanada

- Ta ce babu gudu ba ja da baya, tana bayan dokar da majalisar tarayyar kasar nan ke yunkurin kafawa a kan daidaita soshiyal midiya

Uwargidan shugaban kasa Muhammadu Buhari, Aisha Buhari ta tabbatar da cewa ba za a iya hanata magana ba. Ta sanar da hakan ne a ranar Alhamis 5 ga watan Disamba a birnin Landan.

Uwargidan shugaban kasar an gayyaceta ne ta wayar salula a shirin gidan talabijin na TVC mai suna ‘Journalists Hangout’. Ta yi bayani ne a kan tsokacin da ta yi a kan dokar kafafen sada zaumuntar zamani da majalisar tarayya ke yunkurin kirkirowa, rashin tsaro, talauci da ya addabi kasar nan da kuma tsokaci da ta yi a kan gwamnoni da ministocin kasar nan.

Aisha Buhari ta ce, tana da damar bayyana ra’ayinta kamar yadda kundin tsarin mulkin kasar nan ya bata. An tambayeta ko zata daina magana, “Wa zai hana ni magana? Kowa a kasar nan magana yake yi. Kowa a barshi ya yi magana. ‘Yancin magana duk muna dashi”, ta ce.

KU KARANTA: An harbe wasu samari guda 4 da aka kama sun yiwa budurwa fyade sun kuma kasheta

Da aka tambayeta ko takan tattauna zancen kalubalen da kasar nan ke fuskanta tare da maigidanta a yayin da suke nishadi, uwargidan shugaban kasar ta ce “Babu irin wannan a fadar shugaban kasar, ko da kuwa a ‘dayan dakin’ ne.”

Matar shugaban kasar ta ce, ta san kalubalen da kasar ke fuskantar sun dade suna taruwa. Ta kara da cewa, bata dora laifi kai tsaye a kan gwamnonin ba a yayin da take jawabi ga majalisar koli ta lamurran addinin musulunci a Abuja. “Dukkanmu muna fuskantar kalubale, ko kai shugaba ne ko mabiyi. Babu mai iya zuwa kauyenshi ya yi bacci ido rufe,” in ji ta.

Ta kara da jaddada cewa, tana bayan dokar daidaita kafafen sada zumuntar zamani. “Babu wani hukunci da masu laifin ke fuskanta. Sai kace duk abinda kake so kuma a kyale ka. Ba zamu kuwa samu kasa mai cike da zaman lafiya ba.” Aisha ta kara da cewa.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit.ng

Online view pixel