Babban suna 'Muhammadu' na cikin jerin sunaye 10 da akafi sanyawa jarirai a Amurka wannan shekarar

Babban suna 'Muhammadu' na cikin jerin sunaye 10 da akafi sanyawa jarirai a Amurka wannan shekarar

Shafin 'Babycenter' da ya shahara da tattara sunaye 100 da akafi sanyawa sabbin jarirai maza da matan da aka haifa a kasar ya fitar da na shekarar 2019.

Shafin da ke ilmantar da iyaye wajen tarbiyar ta tattawa sunayen jarirai 600,000 da aka haifa a shekarar 2019.

A wannan karon, an ga abin mamaki idan sunaye biyu da ba'a saba gani ba suka yanki tuta. Babban suna 'Muhammadu' cikin maza da kuma 'Aaliyah' cikin mata.

Suna 'Muhammadu' ne suna mafi shahara a duniya inda jaridar Indepedent ta bayyana cewa akalla mutane milyan 150 ke amfani da sunar.

Editar jaridar Babycenter, Linda Murray ya bayyana cewa: "Suna 'Muhammadu' ya fara shahara a cikin sunaye a Amurka kuma tun lokacin muka san cewa nan ba da dadewa ba zai shiga jerin 10 mafi shahara."

"Musulmai kan zabi suna Muhammadu ga dan fari domin girmama manzon Allah (SAW)."

DUBA NAN: Bayan kwanaki a boye, dan sandan da ya bindige direban mota ya mika kansa ga hukuma

Ga jerin sunayen mata da maza:

Mata:

1. Sophia

2. Olivia

3. Emma

4. Ava

5. Aria

6. Isabella

7. Amelia

8. Mia

9. Riley

10. Aaliyah

Maza

1. Liam

2. Jackson

3. Noah

4. Aiden

5. Grayson

6. Caden

7. Lucas

8. Elijah

9. Oliver

10. Muhammad

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit.ng

Tags:
Online view pixel