An yi asarar rai a wani rikici tsakanin Fulani da Hausawa a Jigawa

An yi asarar rai a wani rikici tsakanin Fulani da Hausawa a Jigawa

Rundunar Yansandan jahar Jigawa ta sanar da tura karin jami’an Yansanda zuwa karamar hukumar Guri domin kwantar da tarzomar da ta tashi a yankin wanda har ta yi sanadiyyar mutuwar mutum daya.

Rahoton kamfanin dillancin labarun Najeriya, NAN, ta bayyana cewa rikicin ya faru ne tsakanin kabilun Hausawa da Fulanin yankin, kamar yadda kaakakin rundunar Yansandan jahar, SP Abdu Jinjiri ya tabbatar.

KU KARANTA: Manyan dalilai 3 da suka sanya ba’a cin naman akuya a jahar Sakkwato

Majiyar Legit.ng ta ruwaito SP Jinjri ya bayyana ma manema labaru a garin Dutse cewa: “Jiya da misalin karfe 4:56 na yamma muka samu rahoton kaurewar rikici a rugar Fulani ta Bodala dake cikin karamar hukumar Guri a tsakanin Hausawa da Fulani.

“An yi wannan rikici ne a daidai kan hanyar Guri-Adiyani, inda Fulani suka Sassari wani bahaushe mai suna Abubakar Dada dan shekara 38, a bayansa, kai da hannuwansa, ba tare da bata lokaci ba aka garzaya da shi zuwa asibitin garin Hadejia, a can Allah Ya yi masa cikawa. A dalilin haka mun kama wani Usman Isah daga rugar Fulani ta Bodala.” Inji shi.

Shi ma shugaban Miyetti Allah reshen jahar Jigawa, Sa’idu Gagarawa ya bayyana cewa rikicin ya samo asali ne bayan wani dan babur ya buge wata Saniya, inda su kuma makiyayan suka kashe dan babur din.

Jami’in watsa labaru na kamar hukumar Guri, Sunsui Doro ya bayyana ma manema labaru cewa baya ga mutuwar Dada, an samu mutane biyar da suka jikkata, ya kara da cewa hankula sun tashi a kananan hukumomin Guri da Kirikasamma, wanda har ya sanya Fulani tserewa daga kauyukansu.

Haka zalika wani mazaunin yankin yace jama’a sun yi ta guna guni a lokacin da ake gudanar da jana’izar mamacin, inda har suka nemi su sauke fushinsu a kan shugaban karamar hukumar Guri daya halarci jana’izar, da kyar aka sulale da shi.

Ku biyo mu a https://facebook.com/legitnghausa

ko a http://twitter.com/legitnghausa

KU LATSA: Hanyar sauko da sabuwar manhajar jaridar Legit.com Hausa cikin sauki

Ga masu shawara ko korafi, a same mu a labaranhausa@corp.legit.com

Sanarwa na musamman: Shafin NAIJ Hausa ya koma Legit Hausa

Source: Legit.ng

Online view pixel