Zaratan Sojojin Najeriya sun karkashe yan Boko Haram, sun ceto mutane da dama

Zaratan Sojojin Najeriya sun karkashe yan Boko Haram, sun ceto mutane da dama

Gangancin gangan ya debi wasu gungun mayakan kungiyar ta’addanci na Boko Haram inda suka yi kokarin kutsa kai cikin sansanin Sojojin Najeriya na bataliya ta 112 dake garin Mafa cikin karamar hukumar Mafa na jahar Borno.

Su dai wadannan mayaka yan ta’adda suna dauke da wasu motocin yaki ne guda biyar a lokacin da tsautsayi ya debesu zuwa wannan sansani a ranar 1 ga watan Disamba, inda ba tare da wata wata ba Sojoji suka yi musu luguden wuta, cikin dan kankanin lokaci sai filin.

KU KARANTA: Baki yan kasar India 18 sun fada hannun yan fashin teku a cikin tafkin Najeriya

Duba da karfin makaman dake hannun Sojojin, sun kashe da dama daga cikin yan ta’addan yayin da sauran suka ranta a na kare “kafa mai naci ban baki ba?”, duk da haka Sojoji basu gajiya ba, sai da suka bi su har cikin daji suka karkashesu.

A karshe artabun, Sojoji sun gano gawarwakin yan ta’addan da suka mutu, biyu daga cikinsu na dauke da jigidar bom, haka zalika yan ta’addan sun zubar da motar yaki 1, samfurin bindigu daban daban, alburusai, kayan karafan yin tiyata, kakin Boko Haram da kuma rigunan sanyi.

Haka zalika a garin Gwoza wasu mata yan kunar bakin wake sun yi kokarin sadadawa cikin sansanin Sojojin Najeriya dake garin dauke da bamabamai, amma cikin ikon Allah Sojojin dake gadin sansanin sun ganesu, kuma suka tashesu daga aiki tun kafin su tayar da bamabaman.

Bugu da kari Sojojin Najeriya sun samu nasara a wani samame da suka kaddamar a wani gida da yan Boko Haram ke ajiye mata da kanan yara a Kotembe cikin karamar hukumar Bama na jahar Borno.

Sojojin sun kaddamar da samamen ne bayan samun bayanan sirri game da ayyukan yan ta’addan, don haka suka nufi kauyen tare da jaruman matasa yan sa kai, tun daga nesa yan ta’adda suka hangi tawagar, sai suka fara harbe harbe.

Amma duk da haka sai da tawagar ta isa har gidan, ko kafin su isa yan ta’addan sun tsere, amma an ceto mata 12 da kanann yara 4, kamar yadda kaakakin Operation Lafiya Dole, Kanal Aminu Iliyasu ya bayyana.

Ku biyo mu a https://facebook.com/legitnghausa

ko a http://twitter.com/legitnghausa

KU LATSA: Hanyar sauko da sabuwar manhajar jaridar Legit.com Hausa cikin sauki

Ga masu shawara ko korafi, a same mu a labaranhausa@corp.legit.com

Sanarwa na musamman: Shafin NAIJ Hausa ya koma Legit Hausa

Source: Legit.ng

Online view pixel