Baki yan kasar India 18 sun fada hannun yan fashin teku a cikin tafkin Najeriya

Baki yan kasar India 18 sun fada hannun yan fashin teku a cikin tafkin Najeriya

Yan fashin cikin ruwa sun kama wani babban jirgin ruwa mallakin kasar HongKong yayin daya ratsa ruwan Najeriya, inda suka yi awon gaba da fasinjojin jirgin su goma sha tara (19), inji rahoton jaridar Sahara Reporters.

Majiyar Legit.ng ta ruwaito kamfanin ARX Maritime dake sa ido a harkar sufurin jirgin ruwa a kasar Hong Kong ne ya tabbatar da satar jirgin ruwan da fasinjojinta gaba daya kamar yadda ta wallafa a shafinta na yanar gizo.

KU KARANTA: Majalisa ta yi kira ga Buhari ya gudanar da kidayar yan Najeriya a 2020

Jirgin mai suna ‘Nave Constellation’ ya fada hannun yan fashin tekun ne a ranar Talata, 3 ga watan Disamba a daidai lokacin daya ratsa cikin tekun Najeriya. Daga cikin fasinjojin jirgin 19 da aka sace, 18 yan kasar Indiya ne, yayin da guda 1 kuma dan kasar Turkiyya.

Sai dai daga bisani masu garkuwan sun saki jirgin, amma sun yi awon gaba da fasinjojin goma sha tara, a yanzu haka jirgin yana hannun dakarun rundunar Sojan ruwan Najeriya, kamar yadda AXM ta tabbatar.

Ofishin jakadancin kasar India dake Najeriya ta tuntubi gwamnatin Najeriya don ganin an shirya yadda za’a ceto mutanen da yan fashin suka yi awon gaba dasu.

A wani labari kuma, rundunar Yansandan Najeriya reshen jahar Bayelsa ta tabbatar da mutuwar wasu miyagun mutane biyu da ake zargi da satar mutane tare da yin garkuwa dasu, ta hanyar banka musu wuta da wasu fusatattun matasa suka yi.

An kama miyagun ne bayan sun yi garkuwa da wasu dalibai guda 3 da suka fito daga kwalejin kiwon lafiya da kimiyya dake Otuogidi, inda jama’a suka kamasu a Otuagala cikin karamar hukumar Ogbia.

Kaakakin rundunar Yansandan jahar, SP Asinim Butswat ya bayyana cewa a ranar Talata, 3 ga watan Disamba aka kama masu garkuwan, amma jim kadan bayan Yansanda sun kamasu ne sai matasan yankin suka kwacesu daga hannunsu, nan take suka banka musu wuta.

Ku biyo mu a https://facebook.com/legitnghausa

ko a http://twitter.com/legitnghausa

KU LATSA: Hanyar sauko da sabuwar manhajar jaridar Legit.com Hausa cikin sauki

Ga masu shawara ko korafi, a same mu a labaranhausa@corp.legit.com

Sanarwa na musamman: Shafin NAIJ Hausa ya koma Legit Hausa

Source: Legit

Online view pixel