Babban Shehi yayi kaca-kaca da jarumar fim da tace zata sha tabar wiwi da Al-Qur'ani

Babban Shehi yayi kaca-kaca da jarumar fim da tace zata sha tabar wiwi da Al-Qur'ani

- Wata jarumar masana'antar Nollywood mai suna Etinosa ta yi barazanar tozarta kur'ani

- Ta wallafa bayanan asusun bankinta tare da barazanar cewa duk wanda ya turo mata kudi, zata cika yunkurinta

- Babban malami kuma jagora a Ansar-Ud-Deen, ya bayyana cewa neman suna jarumar take, amma bai kamata a dinga yada abinda ta yi ba

Wata jarumar masana'antar Nollywood, ta yi barazanar amfani da shafukan kur'ani don ajiye tokar sigarinta, matukar an bata kudi.

Shugaban limamai na Ansar-Ud-Deen, Abdulrahman Ahmad ya mayar da martani ga jarumar. Ya bayyana mata cewa, ta shirya fuskantar sakamakon duk wani aiki da ta yi.

Sanannen malamin ya ce: "Abun tausayi ne a ce, kasar mu na inda take yanzu. Bana son yin tsokaci a kan irin wadannan lamurran saboda a tunani na ba abun tsokaci bane. Amma kuma, wasu na son su yi suna don haka bai kamata mu taimaka musu ba.

"Mummunan labari ne. Tsokacin da bakin ciki nake yinshi. Wannan abun tambaya ne game da tarbiya, a kan me zamu dinga tattaunawa kan irin lamurrannan kuma muna murna? Muna kara yada mummunan rashin natsuwar Wani.

KU KARANTA: Wata sabuwa: 'Yan madigo sun kafa tarihi a duniya, yayin da suka zama jinsi na farko da suka fara haihuwa

"Idan bibul ne ko kur'ani ko kuma wani littafin daban ne, bai kamata mu yada ba. Ko wani abun ya faru da ita, ko bai faru da ita ba.

"Babu shakka na kushe duk wanda zai iya tozarta bibul ko yunkurin wulakanta kur'ani. Ba maganar tattaunawa bace wannan. Wannan yunkurin jarumar ne na tozarta addinan wasu ne. Yafi kalaman kiyayya muni saboda hakan zai iya hargitsa kasar. Wannan ba 'yancin wani mutum bane, ta siffar al'ada ko addinin wasu.

"Kada mu bar rashin natsuwa ya yadu a fadin kasa. Wannan cin mutunci ne ga 'yan Najeriya tare da addinai. Idan har cibiyoyin shari'a basu dau mataki a kan lamarin ba, toh a shirya fuskantar kalubalen da zai biyo baya. Wannan shine ra'ayi na."

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit.ng

Online view pixel