Babbar magana: Sai mun ga bayanka komin daren dadewa - Gargadin 'Yan Shi'a ga Shugaba Buhari

Babbar magana: Sai mun ga bayanka komin daren dadewa - Gargadin 'Yan Shi'a ga Shugaba Buhari

- Kungiyar Musulmi mabiya akidar shi’a ta bayyana damuwarta na cigaba da rike shugabanta da gwamnatin tarayyar Najeriya ke yi

- Kungiyar ta yi hasashen durkushewar gwamnatin shugaba Muhammadu Buhari matukar aka cigaba da tsare shugaban nata

- Kungiyar ta koka da yadda gwamnatin shugaba Buhari ke kara kirkiro laifukan shugaban nasu ta hannun gwamnatin jihar kaduna

Kungiya musulmi mabiya akidar shi’a ta yi kira ga shugaban kasa Muhammadu Buhari da ya saki shugabansu, Sheikh Ibraheem Zakzaky.

A ranar Litinin da ta gabata ne kungiyar ta koka da cigaba da tsare shugaban kungiyar, tare da matarshi da gwamnatin shugaban kasa Muhammadu Buhari ke cigaba da yi.

Kungiyar ta ce ba shakka gwamnatin shugaban kasa Muhammadu Buhari din zata durkushe matukar bata sako musu shugabansu ba.

A takardar da mai magana da yawun kungiyar, Ibrahim Musa yasa hannu, ya jaddada abunda alkalin da yayi shari’ar yace, yana tsoron abunda zai biyo baya idan gwamnatin Najeriya ta cigaba da tsare musu shugabansu.

Alkalin ya ja kunnen gwamnatin Najeriya a kan tsoron abinda zai faru matukar suka ki sakin shugaban kungiyar. Ya jaddada cewa “ Idan wanda ake karar ya rasa rayuwarshi a yayin da yake tsare, wanda ba a fata, hakan zai iya haifar da mutuwar mutane masu yawa da ba a so.”

KU KARANTA: Katafila Sarkin Aiki: Bidiyon El-Rufai yana bawa motoci hannu a babban titin jihar Kaduna

Duk da hakan, shugaban kasa Muhammadu Buhari ya yi biris da wannan jan kunne inda ya cigaba da tsare shugaban. A maimakon sako shugaban, buhari ya cigaba da zakulo wasu zarge-zarge da ake wa Shehin malamin shi’ar da matarshi ta hannu gwamnatin jihar Kaduna, in ji kungiyar.

“Ya kara da jan kunnen ‘yan Najeriya masu fada a ji, a akan cewa wannan halin na gwamnatin tarayya na take dokar kotu babu abinda zai haifar banda rashin iya juya akalar kasar kamar yadda ake so. Wannan take hakkin dan Adam din da karantsaye ga dokokin kotu sun ba wa kungiyar mamaki, ba kadan ba.”

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit.ng News

Online view pixel