Katafila Sarkin Aiki: Bidiyon El-Rufai yana bawa motoci hannu a babban titin jihar Kaduna

Katafila Sarkin Aiki: Bidiyon El-Rufai yana bawa motoci hannu a babban titin jihar Kaduna

- Bidiyon Gwamnan jihar Kaduna yana ba motoci hannu a babban titin jihar Kaduna ya jawo cece-kuce

- Gwamnan ya sauka daga mota ne a tawagarshi, don ba wa mutane hannu sakamakon cushewar titi da ababen hawa

- Wannan lamarin kuwa ya jawo cece-kuce da kuma tsokaci kala-kala daga mutane a kafafen sada zumuntar zamani

Bidiyon Gwamnan jihar Kaduna, Malam Nasir El-Rufai yana daidaita cunkoson motoci a kan babban titin Kaduna zuwa Zaria ya yawaita a kafafen sada zumuntar zamani.

A ranar Lahadi ne dai gwamnan yana kan babbar hanyar ya ga cushewar titin ya yi yawa. A take kuwa ya sauka daga motar da yake ciki tare da tawagarshi kuma ya fara ba masu ababen hawa hannu.

A bidiyon, an hango gwamnan ya sauka daga motarshi kuma ya fara ba masu ababen hawa hannu don samun raguwar cushewar da cunkoson hanyar.

Bazuwar bidiyon a kafafen sada zumuntar zamani ya jawo cece-kuce daga jama’a. A gaskiya ba wannan bane karo na farko da aka ga gwamnan ya sauka daga tawagarshi kuma yana bada hannu a kan titi ba.

KU KARANTA: Hotuna: Jerin matan Kannywood guda 10 da suka samu nasarar fitowa a wata fitacciyar mujalla

A 2018, Gwamnan jihar Kaduna ya sauka daga tawagarshi sakamakon cushewar hanya a babban titin jihar na Gonin Gora.

Ba wannan ne karo na farko da aka saba nuno gwamnan yana irin wannan jan aikin ba, domin kuwa idan ba a manta ba lokacin zabe da rikici ya barke a jihar Gwamnan da kanshi ya dinga fita da jami'an tsaro yana kwantar da tarzoma.

Bayan haka na taba nuno gwamnan ya bazama cikin daji yana farautar 'yan bindiga da suke garkuwa da mutane akan hanyar Kaduna zuwa Abuja.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit

Online view pixel