Hotuna: A karon farko an kirkiri jirgin kasa da yafi jirgin sama gudu a kasar China

Hotuna: A karon farko an kirkiri jirgin kasa da yafi jirgin sama gudu a kasar China

- Wani sabon samfurin jirgin kasa wanda ya fi jirgin sama sauri ya bayyana a kasar China a wannan makon

- Jirgin na amfani da fasahar titi mai maganadisu ko mayen karfe ne don dage shi daga titin shi

- Fasahar kuwa na rage gugar da zaizayar karafuna da ke tsakanin jirgin kasan da titinshi

Wani sabon samfurin jirgi kasa mai tashi kamar jirgi ya zamo abin jinjina a fannin kimiyya da fasaha. Jirgin dai na tashi ne da taimakon maganadisu wanda ke daidaita shi a titin jirgin kasan.

Jirgin kasan ya fi jirgin sama gudu domin gudunshi ya kai 373mph. Gangar jikin jirgin kasan na farko an fara nuna shi ne a wani gari da ke yankin gabas a birnin Qingdao a kasar China a makon nan.

Hotuna: A karon farko an kirkiri jirgin kasa da yafi jirgin sama gudu a kasar China

Hotuna: A karon farko an kirkiri jirgin kasa da yafi jirgin sama gudu a kasar China
Source: Facebook

Kamfanin jiragen kasa na kasar China ne suka kirkiro abun hawa, za a fara samar da shi ne a shekarar 2021.

KU KARANTA: Wani bawan Allah ya bude wajen sayar da abinci da talakawa suke zuwa su ci abinci kyauta ba tare da sun biya ba

Tun a shekarar 2003 kasar China ta fara amfani da titunan jiragen kasa masu amfani da maganadisu ko mayen karfe, don daga jiragen kasa daga titi tare da sanya su tafiya.

Hotuna: A karon farko an kirkiri jirgin kasa da yafi jirgin sama gudu a kasar China

Hotuna: A karon farko an kirkiri jirgin kasa da yafi jirgin sama gudu a kasar China
Source: Facebook

Wannan fasahar kuwa na rage gugar karafunan da ke tsakanin jiragen kasan da kuma titunan. Hakan kuma na ba jiragen kasan damar tafiya da sauri.

Mataimakin babban Injiniya na CRRC, Ding Sansan ya ce, “A misalin tafiya daga Beijing zuwa Shanghai zai dau sa’o’i hudu da rabi a jirgin sama, sa’o’i biyar da rabi a jirgin kasa, amma wannan sabon jirgin zai dauki sa’o’i uku da rabi kacal. CRRC zata gina titin jirgi don gwada jirgin.”

Hotuna: A karon farko an kirkiri jirgin kasa da yafi jirgin sama gudu a kasar China

Hotuna: A karon farko an kirkiri jirgin kasa da yafi jirgin sama gudu a kasar China
Source: Facebook

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit

Online view pixel