Wani bawan Allah ya bude wajen sayar da abinci da talakawa suke zuwa su ci abinci kyauta ba tare da sun biya ba

Wani bawan Allah ya bude wajen sayar da abinci da talakawa suke zuwa su ci abinci kyauta ba tare da sun biya ba

- Wani mawakin kasar Amurka mai suna Jon Bon Jov, ya tallafawa rayuwar mutane ta hanyar ciyar da mabukata

- A gidan cin abincinshi mai suna JBJ, mutanen da ke bukatar taimako kan garzaya don cin abinci matukar sun tallafawa gidan cin abincin

- Babban burin mawakin shine yakar yunwa da rashin tsaro ta bangaren abinci

Wani mawakin kasar Amurka mai suna Jon Bon Jovi, ya saba tallafawa rayuwar mutane da dukiyarshi tun shekaru masu yawa da suka shude. A 2006, an ruwaito yadda ya kirkiro gidauniyar tallafi ta Jon Bon Jovi Soul, wacce ke taimako wajen fatattakar fatara. Bored Panda ta ruwaito yadda gidauniyar ta tallafa wajen bude gidan cin abinci inda mutane ke cin abinci ba tare da an biya ba.

A yayin da aka kaddamar da gidan cin abincin na farko a watan Oktoba 2011, a yankin Red Bank da ke New Jersey. Na biyun kuwa an budeshi ne a 2017 a Toms River.

Daya daga cikin burin matallafin ya hada da yaki da rashin tsaro ta fuskar abinci. Amma kuma duk kwastoman da zai ci abincin kuma ya biya, ana matukar maraba da shi. A gidan cin abincin, wanda zai iya biya ana shawartarshi ne da ya biya $20, wadanda kuma ba zasu iya ba su ba kan taimaka wajen girki.

KU KARANTA: Dr Maimuna: Mata na samun matsalar kwakwalwa idan ba sa saduwa da maza da yawa

Daga bude wajen cin abinci, an ciyar da a kalla abinci kala 105,893. Kashi 54 na cikin abincin duk daga kyautar da mutane ke yi wa gidan cin abincin ne.

A wajen cin abincin, wanda ya fara zuwa ne ake fara zuba wa kuma babu mai ajiye kujera don wani. Sai dai akan fifita talakawa.

Wani abun tunawa shine yadda gidan cin abincin ya ciyar da ma'aikatan gwamnati wadanda suka bar aiki a ranar 21 ga watan Janairu.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel