Dr Maimuna: Mata na samun matsalar kwakwalwa idan ba sa saduwa da maza da yawa

Dr Maimuna: Mata na samun matsalar kwakwalwa idan ba sa saduwa da maza da yawa

- Dr. Kadiri babbar likitar kwakwalwa ce da ke aiki da asibitin Pinnacle a matsayin shugabar asibitin

- Ta bayyana yadda jima'i ke cirewa mata damuwa tare da warkar dasu daga wasu cutukan kwakwalwa da suka hada da ciwon kai

- Ta yi bayanin yadda jima'i ke cire damuwa ga mata tare da kara musu kima, baya ga gyara jiki da yake yi

A ranar Asabar ne wata likitan kwakwalwa mai suna Dr Maymunah Kadiri, ta shawarci matan aure da su yawaita jima'i da mazajensu don rage damuwa tare da samun farin ciki.

Kadiri, shugabar asibitin Pinnacle ta bada wannan shawarar ne a wata tattaunawa da ta yi da manema labarai a garin Legas.

Kamar yadda ta ce, jima'i ba wai gyara jikin mace kawai yake ba, yana da matukar amfani ga lafiyar kwakwalwa.

"A matsayinmu na mata, akwai bukatar mazajenmu su zama aminanmu, matukar muna bukatar lafiyar kwakwalwa ingantacciya. Ilimi ne ya nuna cewa, matan da ke samun jima'i akai-akai basu cika samun damuwa ba idan aka danganta su da wadanda basu samu."

KU KARANTA: Tashin hankali: An kama wani mutumi da ya yiwa akuyoyi guda biyu fyade har suka mutu

"Jima'i na da matukar amfani. Maganin matsanancin ciwon kai ne ga mata. Mace na fadawa damuwa matukar yawan jima'in da take samu ya ragu."

"Jima'i da yawa yana takar rawar gani wajen kara wa mace lafiyar kwakwalwa tare da ingantacciyar rayuwa."

Dr. Kadiri, ta kara da kira ga matan da ke da damuwa da su yawaita yin jima'i, lamarin na kara musu kima da lafiya.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Authors:
Mudathir Ishaq avatar

Mudathir Ishaq Mudathir Ishaq is the head of the Hausa desk at Legit.ng. He studied Industrial Chemistry as first degree at the University of Abuja, Journalism (CSR Specialization) with the Michigan State University and runs MSc Industrial Chemistry from the Nasarawa State University, Keffi. With more than a decade experience in news reporting and content editing, he has interviewed influential personalities. He can be reached on: mudathir.ishaq@corp.legit.ng