Yanzu nan: Lantarki ta yi sanadiyyar mutuwar wasu a kurkukun Ikoyi

Yanzu nan: Lantarki ta yi sanadiyyar mutuwar wasu a kurkukun Ikoyi

Mun samu labari cewa hadarin wuta ya yi sanadiyyar rasuwar mutane rututu da ke tsare a gidan yarin Ikoyi. Wannan mummmunan abu ya auku ne a safiyar Yau Litinin dinnan.

Kamar yadda mu ka samu labari daga jaridar Premiun Times, lantarkin ya hallaka mutane da yawa, wasu da-dama har ila yau sun jikkata a dalilin samun muguyen raunuka.

Hadarin ya auku ne bayan da layukan wuta su ka fara kamawa su na ci, wannan ya yi sanadiyyar jan wasu da ke garkame a cikin wannan katafaren gidan kurkuku da ke jihar Legas.

Kakakin hukumar gidajen yari na Najeriya, Francis Enobore, ya tabbatarwa Manema labarai aukuwar wannan hadari. Sai dai kawo yanzu, babu cikakken bayanin abin da ya faru.

Mista Francis Enobore ya fadawa Majiyar cewa zuwa lokacin, su na cigaba da kokarin bin kadin lamarin ne. Hukumar ta ce daga baya za ta fito ta yi wa Duniya cikakken jawabi.

KU KARANTA: Za a cigaba da garkame iyakoki domin har gobe Benin ba ta tuba ba - FG

Jita-jita ta na zuwa mana cewa akalla mutum biyar su ka rasa rayukansu a hadarin. Bayan haka kuma za a samu fiye da mutane goma da su ka samu raunuka daga jan lantarkin.

Ministan harkokin cikin gida na Najeriya, Rauf Aregbesola, ya yi maza ya yi magana bayan abin ya auku. Mai girma Ministan ya bukaci a binciki abin da ya jawo hadarin dazu.

Ogbeni Rauf Aregbesola ya yi jawabi ne ta bakin Sakatarensa na yada labarai Jane Osuji, a Ranar 2 ga Watan Disamban 2019. Ministan ya ce zai fito ya yi dogon jawabi daga baya.

Gidan kurkukun na Ikoyi ya na cikin manyan gidajen yari da ake da su a kasar nan. Haka zalika ya na cikin tsofaffin gidajen kason da ke tsare da mutane masu laifi sama da 2000.

Idan ku na da wata shawara ko bukatar bamu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewa tare da mu.

Ga masu bukatar manhajar mu na Musulunci sai a bibiyi wannan shafi

https://fb.gg/play/ramadan_ramadan

Asali: Legit.ng

Online view pixel