Mai Tabargaza: Jarumar fim da ta sha tabar wiwi da shafin Bible ta ce a shirye take ta yayyaga Al-Qur'ani idan aka bata

Mai Tabargaza: Jarumar fim da ta sha tabar wiwi da shafin Bible ta ce a shirye take ta yayyaga Al-Qur'ani idan aka bata

- Fitacciyar jarumar fina-finan Kudancin Najeriya Etinosa Idumedia ta sha zagi a wajen mutane bayan ta wallafa wani sabon bidiyo a shafinta na Instagram da ya jawo kace-nace

- Jarumar dai ta wallafa wani bidiyo ne da aka nuno ta tana shan tabar wiwi da shafin littafin Bible, sannan ta bayyana cewa babu komai a jikin shafin sai karya

- Jarumar dai dama ba bakuwa bace wajen jawo kace-nace a shafukan sada zumunta, domin kuwa kwanakin baya ta wallafa wani bidiyonta tsirara a shafinta na Instagram da ya jawo kace-nace

Fitacciyar jarumar fim ta kudancin Najeriya Etinosa Idemudia ta sha zagi daga wajen masoyanta bayan ta wulakanta litaffin Bible sannan kuma ta sha alwashin wulakanta Al-Qur'ani mai girma idan aka bata a wani sabon bidiyo da yake ta yawo a shafukan sadarwa.

A bidiyon, jarumar wacce take haifaffiyar garin Warri ta yaga wani shafi a jikin littafin Bible din inda tayi amfani da shi ta sha tabar wiwi, sannan kuma tace duka karya ce a jikin shafin.

Sai dai kuma wasu daga cikin masoyanta sun nemi da idan har ta isa ta gwada yin wannan cin mutunci da ta yiwa Bible akan Al-Qur'ani mai girma, cikin gaggawa kuwa jarumar ta maida musu martani kamar haka: "Ina bukatar littafin Qur'ani yanzu-yanzu, wace irin magana ce wannan, ku bani Qur'ani yanzu zanyi kaca-kaca da shi a cikin dakika biyu. Su waye ku da har zaku kalubalance da wasu littattafai guda biyu?"

KU KARANTA: Nanfe Joy Jatau: Budurwa mai digiri da ta cire girman kai take wankin mota

To sai dai kuma wannan martani da jarumar ta bayar ya jawo mata zage-zage da Allah wadai a dukkanin bangarori guda biyu na Musulmai da Kirista.

Etinosa ba bakuwa bace wajen jawo kace-nace a shafukan sada zumunta na zamani domin kuwa a kwanakin baya an sha fama da ita bayan ta wallafa wani bidiyo nata tsirara a shafinta na Instagram.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Authors:
Mudathir Ishaq avatar

Mudathir Ishaq Mudathir Ishaq is the head of the Hausa desk at Legit.ng. He studied Industrial Chemistry as first degree at the University of Abuja, Journalism (CSR Specialization) with the Michigan State University and runs MSc Industrial Chemistry from the Nasarawa State University, Keffi. With more than a decade experience in news reporting and content editing, he has interviewed influential personalities. He can be reached on: mudathir.ishaq@corp.legit.ng