Jerin ‘Ya ‘yan Aisha Buhari da Shugaban kasa Muhammadu Buhari

Jerin ‘Ya ‘yan Aisha Buhari da Shugaban kasa Muhammadu Buhari

A yau ne aka cika shekaru 30 da auren Hajiya Aisha Muhammadu Buhari da kuma Sahibarsa, Aisha Buhari. Mun kawo maku jerin Iyalin da shugaban kasar ya samu tare da Mai dakinsa.

1. Halima Buhari

An haifi Halima-Sheriff ne a karshen shekarar 1990. Halima ta yi karatunta a gida Kaduna da kasashen ketare inda ta je har Kwalejin Bellerby da Jami’ar Leicester duk da ke Ingila. Halima ta zama Lauya a tsakiyar shekarar 2016, kuma ta na auren Babagana Muhammad Sheriff tun 2012.

2. Yusuf Buhari

Yusuf Buhari ne babban ‘Da kuma Namijin da kurum Hajiya Aisha Buhari ta haifa a Duniya. An haifi Yusuf ne shekaru 27 da su ka wuce. Yusuf ya yi karatu jami’ar Surrey ta Ingila tare da ‘Yanuwansa, ya kuma yi bautar kasa a gida. Shi ne ‘Da namijin da Buhari ya mallaka a yanzu.

KU KARANTA: Yau shekaru 30 da auren Shugaba Buhari da Aisha Buhari

3. Zahra Buhari

Zahra Buhari-Indimi ce wanda ta fi fice a cikin ‘Ya ‘yan shugaban kasar. Jama’a sun fara sanin Zahra ne daf da zaben 2015. Zahra ta yi karatu ne tare da ‘Yanuwanta. An haifi Zahra ne a Ranar 18 ga Disamban 1994. Ta auri Ahmed Muhammad Indimi ta na da shekaru 22 a Duniya.

4. Aisha Buhari

Aisha Buhari ce ‘Diyar Uwargidar Najeriya Hajiya Aisha Buhari ta hudu. An fi kiran Aisha da Hanan domin a sakaya sunan Mahafiyarta. An haifi Hannan ne a karshen Agustan 1998. Wannan ya na nufin ‘Yar karamar Aisha Buhari ta na da shekaru 21. Hannan ta na sha’awar daukar hoto.

5. Amina Buhari

Amina Buhari mai shekaru 15 da haihuwa ce ‘Yar autar shugaba Buhari da Mai dakinsa. Kamar yadda Jaridar Premium Times ta taba kawo rahoto kwanaki, ana yi wa ‘Yar autar da Noor. Noor da ‘Yaruwarta Hannan ba su yi aure ba tukuna. A da can, su na karatunsu ne a Garin Kaduna.

Idan ku na da wata shawara ko bukatar bamu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewa tare da mu.

Ga masu bukatar manhajar mu na Musulunci sai a bibiyi wannan shafi

https://fb.gg/play/ramadan_ramadan

Source: Legit.ng

Online view pixel