Dalilinmu na fara gina sabuwar jami'ar sufuri a garin Daura - NRC

Dalilinmu na fara gina sabuwar jami'ar sufuri a garin Daura - NRC

A ranar Litinin ne Daraktan kula da hukumar harkokin jiragen kasa (NRC) da ke karkashin ma'aikatar sufuri ta tarayya, Injiniya Mohammed Babakobi, ya ce an dauki Daura ne don gina sabuwar Jami'ar sufuri saboda dabarun shawo kan matsalar sufurin jiragen kasa da suke tasowa a yankin.

Kamar yadda yace, za a samu titin jirgin kasa da zai tashi daga Kano zuwa Kaduna wanda zai ratsa ta cikin Katsina. Sai kuma titin jirgin kasa na kasa da kasa da zai fara daga Katsina zuwa Jibia a jamhuriyar Nijar.

Ya ce jami'ar zata fara aiki ne a 2021 kuma ana tsammanin zata fara karatuttuka tare da horarwa a bangaren sufurin jiragen kasa.

Kamar yadda ya ce, ma'aikatar na kokarin aiki da ma'aikatar ilimi da kuma hukumar kula da harkokin jami'o'i ta kasa (NUC), a yunkurinsu na fadada yanayin karatun don habakar bangaren sufurin jiragen kasa wanda aka nuna wa halin ko in kula a baya.

Babakobi na wadannan kalamai ne a daidai lokacin da wasu 'yan Najeriya ke korafi a kan rashin dacewar gina jami'ar a garin Daura, tare da bayyana yin hakan a matsayin aikin 'riya' domin kawai a burge shugaban kasa, Muhammadu Buhari, wanda haifaffen garin Daura ne.

DUBA WANNAN: Hotunan gidaje 10 mafi kyau da tsada a Najeriya

Tuni Legit.ng ta wallafa rahoton cewa shugaba Muhammadu Buhari ya kaddamar da fara ginin sabuwar jami'ar koyar da ilimin Sufuri a mahaifarsa da ke Daura, jihar Katsina.

An yanki filin gina jami'ar ne a karamar hukumar Sandamu ta jihar Katsina.

Hadimin shugaba Buhari a kan sabbin kafafen yada labarai, Bashir Ahmad, ya bayyana cewa: "An kafa tarihi! Shugaba Muhammadu Buhari ya kaddamar da shirin gina sabuwar Jami'ar Sufuri a Daura."

Kamfanin gine-ginen kasar Sin wato China Civil and Construction Company (CCECC), ce za ta gina jami'ar irinta na farko (a Najeriya)."

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel