Gwamna Nasir El-Rufai ya rattafa hannu kan kasafin kudin 2020 na jahar Kaduna

Gwamna Nasir El-Rufai ya rattafa hannu kan kasafin kudin 2020 na jahar Kaduna

Gwamnan jahar Kaduna, Malam Nasir Ahmad El-Rufai ya rattafa hannu kan dokar kasafin kudin shekarar 2020 a ranar Litinin, 2 ga watan Disamba a ofishinsa dake fadar gwamnatin jahar, gidan Sir Kashim Ibrahim.

Gwamnan ya rattafa hannu kan kudurindokar ne a gaban kaakakin majalisar dokokin jahar, mataimakin kaakakin majalisar dokokin jahar, mataimakiyar gwamnan jahar, shugaban ma’aikatan fadar gwamnatin jahar, sakataren gwamnatin jahar da sauran yan majalisu.

KU KARANTA: Yan ta’adda sun bude ma kiristoci wuta a coci, sun kashe 14 a Botswana

Sai dai a yayin da take aikin tantance kasafin kudin, majalisar ta kara yawan kasafin kudin daga naira biliyan 257.9 zuwa 259.25, kuma wannan shine abinda suka aika ma mataimakiyar gwamnan jahar Kaduna, Hadiza Balarabe yayin da take mukaddashiyar gwamnan jahar a ranar 15 ga watan Nuwamba.

A yayin rattafa hannun, Gwamna El-Rufai ya bayyana gamsuwarsa da kasafin, inda yace kasafin ya kunshi kashi 71, watau kimanin naira biliyan 184.1 ne don gudanar da manyan ayyuka, yayin da kudaden albashi da fansho zasu kwashe naira biliyan 75 ne kacal.

Bugu da kari, dokar kasafin kudin shekarar 2020 ta tanadi naira biliyan 75.44 don kashe ma bangaren ilimi da kiwon lafiya ta hanyar samar da manyan ayyuka, yayin da gwamnati za ta kashe naira biliyan 68.5 wajen gina gidaje da sauran ababen more rayuwa.

A wani labarin kuma, wani jarumi daya shahara wajen kama barayi da miyagu a jahar Kaduna, Shehu Musa Aljan ya sake samun nasara yayin da yayi arangama da wasu gungun yan bindiga da suka tattara shanun mutane da nufin haurawa dasu gadar Kaduna.

Barayin sun sato dabbobin ne daga kauyen Rijana dake kan hanyar Kaduna zuwa Abuja, inda suka yi kokarin tserewa dasu ta kan gadar rafin Kaduna, amma suka ci karo da Aljan.

A dalilin wannan kicibus da suka yi da Aljan, barayin sun yi asarar dabbobinsu gaba daya, bindgunsu guda biyu kirar AK 47, sa’annan Aljan ya samu nasarar kama wani kasurgumin barawo daga cikinsu.

Ku biyo mu a https://facebook.com/legitnghausa

ko a http://twitter.com/legitnghausa

KU LATSA: Hanyar sauko da sabuwar manhajar jaridar Legit.com Hausa cikin sauki

Ga masu shawara ko korafi, a same mu a labaranhausa@corp.legit.com

Sanarwa na musamman: Shafin NAIJ Hausa ya koma Legit Hausa

Asali: Legit.ng

Online view pixel