A garin kokarin tserewa, mai laifi ya kashe jami’in Dansanda a jahar Katsina

A garin kokarin tserewa, mai laifi ya kashe jami’in Dansanda a jahar Katsina

Wani mamuguncin yaro dan shekara 22, Yusuf Lawal ya halaka wani jami’in rundunar Yansandan Najeriya mai suna Kofur Musa Isiyaku a yayin da Dansandan ya yi kokarin kamashi da hannunsa.

Jaridar Punch ta ruwaito a ranar Juma’ar data gabata ne aka gurfanar da Lawal gaban wata babbar kotun majistri dake zamanta a garin Katsina, inda ake tuhumarsa da laifin kashe Dansanda Isiyaku har lahira a kokarinsa na hana Dansandan ya kama shi.

KU KARANTA: Yan ta’adda sun bude ma kiristoci wuta a coci, sun kashe 14 a Botswana

Majiyarmu ta ruwaito Lawal ya yi amfani fa almakashi ne wajen kashe dansandan, inda ya burma masa ita a cikinsa da kuma kirjinsa, wanda a sanadiyyar haka jami’in dansandan ya rasa rayuwarsa, a karamar hukumar Malumfashi ta jahar Katsina.

A ranar 5 ga watan Nuwambar 2019 aka aika kofur Isiyaku gida mai lambya 22, layin yan bori cikin garin Malumfashi da nufin kama Lawal wanda aka samu rahoton ya shiga unguwar da nufin yin sata tare da abokansa, da misalin karfe 10:30 na dare.

Shigarsu layin keda wuya sai suka ci karo da Lawal da abokinsa A.T, nan take Isiyaku ya yi kan Lawal da nufin kama shi, amma sai Lawal ya zaro almakashi ya burma masa, daga nan aka garzaya da shi zuwa babban asibitin garin Malumfashi, amma bai sha ba.

Da wannan laifin ake tuhumar Lawal, wanda idan aka kamashi da laifi zai fuskanci hukunci kamar yadda sashi na 189 na kundin hukunta manyan laifuka ta tanadar, bugu da kari Lawal ya amsa laifinsa yayin da Yansanda suke bincikensa.

Bayan sauraron tuhume tuhumen da ake yi ma Lawal, Alkalin kotun, mai sharia Fadila Dikko ta dage karar zuwa ranar 30 ga watan Janairun shekarar 2020, sa’annan ta bada umarnin a garkame mata shi.

Ku biyo mu a https://facebook.com/legitnghausa

ko a http://twitter.com/legitnghausa

KU LATSA: Hanyar sauko da sabuwar manhajar jaridar Legit.com Hausa cikin sauki

Ga masu shawara ko korafi, a same mu a labaranhausa@corp.legit.com

Sanarwa na musamman: Shafin NAIJ Hausa ya koma Legit Hausa

Asali: Legit.ng

Online view pixel