Yusuf Buhari ya shigar da karar matarsa a kan sauya wa yara makaranta

Yusuf Buhari ya shigar da karar matarsa a kan sauya wa yara makaranta

A ranar Juma'a ne wani mutum mai suna Yusuf Buhari, ya maka matarshi mai suna Hadiza Muhammad, gaban kotun shari'a da ke zama a Magajin Gari, jihar Kaduna, a kan sauyawa yaransu mata biyu makaranta ba tare da saninshi ba.

Buhari, wanda ke zaune a birnin Kaduna, ya mika kararshi ne a gaban kotun ta hannun lauyanshi, Sani Shehu. Ya bayyana yadda matarshi ta mayar da yaransu mata biyu gidan iyayenta kuma ta canza musu makaranta daga wacce ya sanyasu.

Lauyanshi ya ce, watanni shida kenan da Muhammad ta hana mijinta ganin yaranshi kamar yadda kotu ta umarta, duk da kuwa suna matsayin mata da miji.

Ya roki kotun da ta umarci matar da ta mayar da yaran makarantar da mahaifinsu ya sa su kuma ta mayar dasu gidan mahaifinsu, duba da har yanzu suna matsayin mata da miji ne.

Mai kare kanta, ta bakin lauyanta, Adam Hassan, ta ce shari'ar musulunci ta aminta da mace ta tafi duk inda zata tare da 'ya'yanta.

DUBA WANNAN: Ina son zama 'yar kasuwa kamar Dangote - Jaruma Sadiya Kabala

"Idan zata iya tafiya dasu wajen da ya dace, ba mai nisa daga mahaifinsu ba, shari'a ta aminta. Duk da sun samu 'yar hayaniya, har yanzu matarshi take," lauyan yace.

Kamfanin dillancin labaran Najeriya (NAN) ya ruwaito yadda Muhammad tanemi saki daga mijinta ta hanyar maka shi gaban kuliya amma sai wata babbar kotu ta hana.

Bayan sauraron duk bangarorin, Alkali Murtala Nasir ya dage sauraron shari'ar zuwa 6 ga watan Disamba.

Ya umarci lauyoyin da su zo da kwafin shari'ar babbar kotun a zama na gaba.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel