Labari mai dadi: Buhari zai gina sabuwar jami’ar rundunar Sojan sama a Bauchi

Labari mai dadi: Buhari zai gina sabuwar jami’ar rundunar Sojan sama a Bauchi

Gwamnatin Najeriya a karkashin jagorancin shugaban kasa Muhammadu Buhari za ta gina katafarem jami’ar rundunar Sojan sama a garin Bauchi na jahar Bauchi kamar yadda babban hafsan sojan sama ya tabbatar.

Jaridar Punch ta ruwaito babban hafsan sojan sama, Air Marsharl Saddique Abubakar ya bayyana haka yayin da yake amsa godiyar da gwamnan jahar Bauchi, Sanata Bala Muhammad ya yi masa game da kawo jami’ar jahar Bauchi.

KU KARANTA: Sojojin saman Najeriya sun zazzaga ma yan ta’adda ruwan wuta a jahar Borno

A jawabinsa, Gwamna Bala ya jinjina ma Sadiqque Abubakar, inda ya bayyana shi a matsayin dan kasa nagari mai kishin asalinsa ta hanyar kawo musu abubuwanc cigaba a jahar. Daga cikin abubuwan da babban sojan ya kai jahar Bauchi akwai cibiyar aikin Sojan sama na musamman dake garin Bauchi.

Da yake mayar da amsa godiyar gwamnan, babban hafsan sojan yace shirye shirye sun yi nisa don kafa jami’ar rundunar Sojan sama a Bauchi, haka zalika rundunar sojan sama za ta gudanar da aikin gyara tare da fadada jirgin sama dake garin Azare.

A wani labarin kuma, rundunar Sojin Najeriya ta sanar da cewa jiragen yakinta dake aikin tabbatar da tsaro a yankin jahar Borno a karkashin aikin Operation Lafiya Dole sun tarwatsa wasu manyan motocin yakin yan ta’addan Boko Haram guda biyu, tare da kashe mayakan dake ciki.

Rundunar ta samu wannan nasara ne a kauyen Borgozo dake jahar Borno, inda ta hangi yan Boko Haram suna tafiya a cikin motoci guda biyu, nan da nan ta tura jiragen yakinta ya sauke musu ruwan bala’i, kowa ya mutu a ciki.

Kaakakin rundunar, Ibikunle Daramola ne ya tabbatar da haka cikin wata sanarwa daya fitar a ranar Juma’a, 29 ga watan Nuwamba a babban birnin tarayya Abuja, inda yace wannan nasara ta samu ne a daidai lokacin da jiragen ke baiwa Sojojin kasa tsaro ta sama a yayin da suke artabu da yan ta’adda a yankin.

Ku biyo mu a https://facebook.com/legitnghausa

ko a http://twitter.com/legitnghausa

KU LATSA: Hanyar sauko da sabuwar manhajar jaridar Legit.com Hausa cikin sauki

Ga masu shawara ko korafi, a same mu a labaranhausa@corp.legit.com

Sanarwa na musamman: Shafin NAIJ Hausa ya koma Legit Hausa

Source: Legit Nigeria

Online view pixel