Duniya ina zaki damu: An tsinci gawar karamar yarinya da ta kashe kanta da kanta

Duniya ina zaki damu: An tsinci gawar karamar yarinya da ta kashe kanta da kanta

Wata karamar yarinya yar shekara 9 ta aikata ma kanta sabalikita bayan ta kashe kanta da kanta a gidan da ake rikonta dake rukunin gidajen Ankpa, a cikin garin Makurdi, babban birnin jahar Benuwe.

Jaridar Daily Trust ta ruwaito lamarin ya faru ne da sanyin safiyar Laraba, 27 ga watan Nuwamba, inda aka tsinci gawar karamar yarinyar a cikin bandaki, kamar yadda rundunar Yansandan jahar ta tabbatar.

KU KARANTA: PDP ta yi ma INEC wankin babban bargo, ta nemi Mahmud Yakubu ya yi murabus

Kaakakin rundunar Yansandan jahar, PPRO, DSP Catherine Anene bayyana cewa da misalin karfe 11:30 na safiyar Laraba aka kai musu rahoton tsintar gawar yarinyar, inda tace yarinyar mai suna Abah Maria ta rataye kanta ne a cikin bayi.

Kaakaki Anene ta ce tuni sun mika gawar yarinyar zuwa dakin ajiyan gawarwaki na asibitin St Theresa, sa’annan an kaddamar da bincike a kan musabbaabin lamarin, amma dai tace basu kama kowa da hannu cikin lamarin ba.

Koda majiyarmu ta kai ziyara gidan domin jin ta bakin yan uwan yarinyar, ta tarar da wasu yara, amma basu yarda sun yi magana da yan jaridu ba, inda suka ce mahaifiyarsu ce kadai za ta iya yin bayani yadda ya kamata.

A wani labarin kuma, akalla mutane hudu ne suka mutu a sanadiyyar fashewar wata bututun iskar gas dake unguwar Aduke, cikin karamar hukumar Ifelodun na jahar Legas.

Wannan ibtila’I ya faru ne da sanyin safiyar Alhamis, 28 ga watan Nuwamba, inda baya ga halaka mutane hudu, akalla mutane 50 kuma sun samu munanan rauni a sanadiyyar gobarar.

Rahotanni sun bayyana cewa daga cikin mutanen da suka mutu akwai kananan yara guda biyu. Sai dai shugaban hukumar bada agajin gaggawa na jahar Legas, LASEMA, Olufemi Oke-Osanyintolu ya bayyana cewa mutane 23 ne suka jikkata.

Ku biyo mu a https://facebook.com/legitnghausa

ko a http://twitter.com/legitnghausa

KU LATSA: Hanyar sauko da sabuwar manhajar jaridar Legit.com Hausa cikin sauki

Ga masu shawara ko korafi, a same mu a labaranhausa@corp.legit.com

Sanarwa na musamman: Shafin NAIJ Hausa ya koma Legit Hausa

Source: Legit.ng

Online view pixel