Sheikh Dahiru Usman Bauchi yayi kira ga Barrack Obama da Sarauniyar Ingila su dawo addinin Musulunci na kakanninsu

Sheikh Dahiru Usman Bauchi yayi kira ga Barrack Obama da Sarauniyar Ingila su dawo addinin Musulunci na kakanninsu

- Shahararren malamin addinin musulunci, Sheikh Dahiru Usman Bauchi, ya yi kira ga Obama da Sarauniyar Ingila zuwa musulunci

- Shehin malamin ya jawo hankulansu ne da irin daukakar da Allah ya yi musu na mulki da isa a fadin duniyar nan

- Ya bayyana musu cewa, hanyar godiya ga Allah a kan baiwar da ya yi musu itace karbar kalmar Allah da manzonsa

Sanannen malamin addinin musuluncin nan, Sheikh Dahiru Usman Bauchi, ya yi kira da babbar murya ga tsohon shugaban kasar Amurka, Barrack Obama da Sarauniyar Ingila Elizabeth da sauran kiristoci da su dawo addininsu na Islama.

Sheikh Dahiru Bauchi yayi kiran nan ne a ranar Larabar da ta gabata, lokacin da yake zantawa da manema labarai a gidansa da ke Bauchi, don mika sakon ban gajiya ga wadanda suka halarci Maulidin bana.

Shehin malamin ya ce, “Ina kira ga Barrack Obama, tsohon shugaban kasar Amurka da ya duba girman Allah, ya dawo addinin kakansa. Ya kara da duba baiwar da Allah ya yi mishi, ta yadda ya mulki kasa kamar Amurka duk da kuwa yana dan Afirka."

KU KARANTA: Kyawawan Hotuna: Wasu ma'aurata Hausawa da suka yi auren soshiyal midiya sun bayyana labarin soyayyar su mai ban mamaki

“Hakazalika kuma ya kammala lafiya kalau. Ga wani ko shekaru hudu baiyi ba amma ana kokarin tsigeshi. Dukkan ‘yan uwanka musulmi ne kuma wannan baiwar da Allah ya yi maka, yakamata ka dawo bautarshi. Zamuyi matukar farin ciki idan muka ganka a addinin musulunci.”

Babban shugaban darikar Tijjaniyar, ya yi kira ga Sarauniyar Ingila, Elizabeth. Ya ce, “Ku isar da sakona ga sarauniyar Ingila. Ta dubi girman Allah ta dawo musulunci domin addinin kakanninta ne. Allah ya yi miki baiwa mai tarin yawa. Kin mulki kasar Ingila tun kina karama. Sama da shekaru 60 kika yi kina mulki. Babu wani morewa da zaki yi a halin yanzu da ya wuce ki rungumi addinin Allah.”

Babban malamin ya kammala da roka musu Allah ya yi musu arziki da addinin musulunci da manzo SAW ya zo dashi.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit Nigeria

Online view pixel